Gwamnatin Tarayya Tace Zata Sa Kafar Wando Daya Da Ma'aikatan Da Basa Zuwa Aiki
- Gwamanatin tarayya tace zata bullo da hanyar da zata magance rashin zuwa aiki da ma'aikatan gwamnati keyi
- Shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya tace sabon shirin lura da ma'aikata ta intanet zai taimaka sosai wajen magance matsalolin rashin zuwa aiki.
- Shugaban ma'aikatan gwamnati tace dole a magance matsal-tsalun rashin ingancin aiki a tsakanin ma'aikatan gwamnatin tarayya da ake ganin sunyi kaurin suna
Abuja: Gwamnatin tarayya ta kammala shirye-shiryen sanya ido kan yadda ma’aikatan gwamnati ke gudanar da ayyukansu a fadin kasar nan ta hanyar intanet dan inganta aikinsu.
Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dokta Folashade Yemi-Esan wadda ta bayyana hakan jiya a Abuja, ta ce za a gudanar da wani tsari na “Farko-zuwa-karshe” don bin diddigin ayyukan ma’aikata.
Yemi-Esan wanda ta ke magana a yayin taron masu ruwa da tsaki kan aiwatar da tsarin gudanar da Aiyuka na Zamani PMS, ga ma’aikatan gwamnatin Tarayya, in da ta ce aikin zai taimaka wajen magance matsal-tsalun da suka shafin ma'aikatan gwamnati.
"Ku Wuce Ɗaki": Wani Mutumi Ya Sunkuci Matarsa Yayin da Ta Kai Masa Ziyarar Bazata, Bidiyon Ya Ja Hankali
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ta bayyana takaicin yadda ma’aikatan gwamnati su kai kaurin suna wajen rashin zuwa aiki, da rashin cika ka’idojinta,. Tace kuma dole ne labari ya canza a gaba.
Ta koka da yadda kasar Kenya da ta fara aikin kafa hukumomi a daidai lokacin da Najeriya ta tai nisa da nata amma basu kai na kasar Kenya ci gaba ba.
"Bai kamata mu yi kasa a gwiwa ba wajen fahimtar cewa isar da manufofin gwamnati ya dogara sosai kan ma'aikatan da ke cimma manufofinsu daban-daban," in ji ta.
A nasa jawabin shugaban hukumar kula da ma’aikatan gwamnatin tarayya Tukur Bello ya bada tabbacin hukumar zata rungumi PMS tare da baiwa OHCSF duk wani tallafi da ya kamata. Rahotan Leadership
Darakta a Sashen Gudanar da Aiyuka na OHCSF, Bosede Olaniyi a cikin jawabinta na dabarun aiki daPMS, ta bayyana cewa PMS ta samu ne saboda bukatar bunkasa ma'aikatan gwamnati.
Gwamnatin Tarayya Zata Soke Yiwa Ma'aikatan Gwamnati Tarayya Jarabawa karin Grima
Gwamnatin tarayya ta ce nan ba da jimawa ba za ta kawar da jarabawar neman karin girma ga ma’aikatan gwamnati, kamar yadda jaridar Bussinesday ta rawaito
Dasuki Arabi, babban darakta na ofishin sake fasalin ma’aikatan gwamnati (BPSR) ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a taron tattaunawa na mako-mako da yan jarida a fadar shugaban kasa a Abuja.
Asali: Legit.ng