Mai Sayar da Kayan Marmari Yaki Karban Sabon Kudin Da CBN Ya Fito Dashi, Yace Jabu Ne

Mai Sayar da Kayan Marmari Yaki Karban Sabon Kudin Da CBN Ya Fito Dashi, Yace Jabu Ne

  • Wani mai sayar da 'ya'yan itace ya ki karban sabon takardar kudin Naira da babban bankin Najeriya CBN ya bullo da shi.
  • A wani faifan bidiyo da Mama ta wallafa a ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba, mai sayar da ’ya’yan itacen ya ce bai san sabon kudin Naira ba.
  • Matakin nasa ya haifar da martani tsakanin masu amfani da TikTok wasu daga cikin wadanda suka goyi bayan mutumin yayin da suka ce har yanzu bayanan ba su yi yaduwa ba.

Masu amfani da TikTok suna maida martani kan wani faifan bidiyon wani mai siyar da kayan marmari da ya ki amincewa da ya karbi sabon kudin Naira na CBN.

An dauki mai siyar da 'ya'yan itacen a cikin wani faifan bidiyo da ya yadu sosai a ranar Alhamis, 15 ga Disamba bayan wani mai amfani da TikTok da aka sani da Mama ya wallafashi

Kara karanta wannan

Wani Miji Ya Maka Matarsa Wajen 'Yan Sanda Kan Kasa Bayanin Yadda Ta Kashe N5m Da Ya Bata

Tik-Tok
Bazan Karba Ba: Mai Sai da Yan Itace Taki Karban Sabon Kudin Da CBN, Ya Fito Dashi Tace Jabu Ne Hoto: TikTok/@dherbie10
Asali: UGC

Bidiyon mai tsawon dakika 21 kacal ya isa ya nuna yadda mai sayar da ’ya’yan itace ke shakkar cewa sabbin takardun Naira na sahihai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mama na kan hanyar wucewa ta yanke shawarar siyan kayan marmari wanda ta gani ana siyarwa a bakin titi.

Mai sai da kayan marmarin ya hada ya kai mata bakin mota, yayin da mama take bashi kudin, mai saida kayan marmarin da yace.

"Ni gaskiya basan wannan kudin ba bazan karba ba."

mama tace:

"Ka karba, sune sabin kudin da babban banki ya canjawa fasali".

Daga karshe dai bai karbi kudin ba, sai wanda aka sani na da suka bashi.

Hakan ya haifar da cece-cece kuce tsakanin masu amfani da TikTok.

Kalli bidiyon a kasa:

Kara karanta wannan

Majilissar Dokokin Kasa A Nigeria ta Ce Babban bankin Kasa Ya Tsaya Da Batun Cire Kudi Tukunna

Wata ma'abociyarmu, Aisha Abdullahi Barde ta bayyanawa Legit cewa;

"Yanxu na dawo daga wani shago siyayya yaki amsa yace jabune"

Martani daga masu amfani da TikTok

@Faithy ya ce:

"yasin ko nice bazan karba, sabida a hannunki na fara ganinta."

@Love Berry a nasa sharhi yace:

"Mutane na kin wannan kudin."

@Ndeejnr ya ce:

"to yasin nima jiya haka ya faru dani"

@akametalu said:

"Sabbin kudin aka ban a banki, amma dana je gida mahaifiyata ta ce jabu ne.

Dalibi ya zama sanannen mai siyar da 'ya'yan itace

A wani labarin mai kama da wanna, Legit.ng ta rawaito cewa wani dalibi dan Najeriya ya zama mai sayar da kayan marmari saboda yajin aikin ASUU .

Matashin ya ce ya fara sana’ar sa ne a lokacin da ake fama da cutar Covid-19 amma abin ya kara Bunkasa saboda yajin aikin.

Ya ce yana so ya ci gaba da fadada kasuwancinsa saboda sha’awarsa ta sha’awar ilimi ta ragu..

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida