Majalisar Dokokin Kebbi Ta Ayyana Kujerun Tsohon Kakakinta Da Wasu 3 a Matsayin Babu Kowa
- Majalisar dokokin jihar Kebbi na shirin maye gurbin wasu mambobinta hudu inda ta saka kujerunsu a kasuwa
- Magatakardar majalisar ya ayyana kujerunsu a matsayin ba kowa bayan sun sauya sheka zuwa PDP
- Yan majalisar sun zargi gwamnatin jihar da kokarin bi ta kan abokan hamayya musamman yan PDP
Kebbi - Majalisar dokokin jihar Kebbi a taronta na ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba ta saka kujerun tsohon kakakinta, Samaila Abdulmumini Kamba da wasu mambobi uku a kasuwa kan sauya sheka da suka yi zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Sauran mambobin da abun ya shafa sune Muhammad Buhari Aliero, Samaila Salihu Bui da Habibu Labbo Gwandu.
Daily Trust ta rahoto cewa an tsige Kamba daga matsayin kakakin majalisar a shekarar da ta gabata kan zargin cewa yana biyayya ga kungiyar Sanata Adamu Aliero.
An zabi Biu a matsayin abokin tafiyar dan takarar gwamnan PDP bayan ya sauya sheka daga APC.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Magatakardar majalisar, Usman Ahmed Bunza, a wata sanarwa da ya saki, ya ce hukuncin saka kujarun a kasuwa ya yi daidai da sashi na 109 na kundin tsarin mulkin Najeriya.
Yan majalisa sun zargi gwamnatin Kebbi da bi ta kan yan adawa
Yan awanni kafin ayyana kujerun a matsayin babu kowa, mambobin majalisar hudu a wani jawabin manema labarai sun koka kan shirin dakatar da su.
Sanarwar ta ce:
"Gwamnati ta kammala shiri don bi ta kan masu adawa a majalisar da kudirin dakatar da mu.
"Shirin shine a shafe yan adawa musamman mambobin PDP a majalisar, ta hanyar tsoratarwa da siye wasu wasu marasa kishin majalisar da kudi don cimma wannan manufa."
Mun fi bukatar Tinubu fiye da yadda yake bukatarmu, jigon APC
A wani labarin, wani babban jagoran jam'iyyar APC mai mulki, Alhaji Onilu ya yi kira ga al'ummar Najeriya a kan su yi tururuwa don zaban Asiwaju Bola Tinubu a zaben 2023.
Onilu ya bayyana cewa yan Najeriya sun fi bukatar Tinubu fiye da yadda shi yake bukatarau don lashe babban zaben shugaban kasa na 2023.
Ya kuma jaddada cewar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi namijin kokari wajen kawo ci gaba a kasar nan.
Asali: Legit.ng