An Gano Wurin Kera Bama-Bamai Mafi Girma a Kudu Maso Gabas, Yan Sanda Sun Yi Martani

An Gano Wurin Kera Bama-Bamai Mafi Girma a Kudu Maso Gabas, Yan Sanda Sun Yi Martani

  • Jami'an rundunar yan sandan jihar Ebonyi sun gano babban wurin kera bama-bamai mafi girma a Najeriya
  • Rundunar yan sandan ta bayyana cewa jami'anta ne suka gano wurin a jihar Ebonyi bayan samun bayanai daga wasu yan kwarmato
  • A cewar yan sandan, an sheke mambobin kungiyar yan awaren IPOB da na Eastern Security Network biyu da ke gudanar da masana'antar

Ebonyi - A ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba, rundunar yan sandan jihar Ebonyi ta ce ta gano wani babban masana'antar kera bama-bamai a yankin kudu maso gabas jaridar The Nation ta rahoto.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Ebonyi, Chris Anyanwu, ya bayyana cewa an gano masana'antar wanda mambobin kungiyar IPOB da takwaransu na Eastern Security Network (ESN) ne ke gudanarwa bayan samun kwarmato kan ayyukan kungiyar.

Kara karanta wannan

Da walakin: Ra'ayoyin jama'a game da hukuncin da aka yankewa Sheikh Abduljabar

Shugaban yan sandan Najeriya
An Gano Wurin Kera Bama-Bamai Mafi Girma a Kudu Maso Gabas, Yan Sanda Sun Yi Martani Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta rahoto cewa Anyanwu ya tabbatar da cewar yan sanda sun samu bayanai abun dogaro kan ayyukan miyagun a Obegu, wani iyaka tsakanin kananan hukumomin Onicha-Isu da Ishielu na jihar Ebonyi.

An kashe mutum biyu tare da kama kwamadojin masana'antar bama-baman

Anyanwu a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa mambobin haramtacciyar kungiyar sun fafata da jami'an yan sanda inda aka kashe mambobin IPOB/ESN biyu tare da kama wasu kwamandojinsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar ta ce

"An yi gaggawar zuwa wurin kuma da taimakon tawagar jami'an tsaro na yankin Ohaukwu an yi nasarar kama Sunday Ubah wanda aka fi sani da Bongo, kwamandan IPOB/ESN na jihar Ebonyi.
"Wanda ya bayar da bayanan sirri game da ayyukan miyagun da fari ya yi ikirarin cewa shine kakakinsu kuma dan Umunnochi a karamar hukumar Isuikwuato da ke jihar Abia.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Halaka Abu Na-Iraqi da Abu-Na Masari, Gawurtattun 'Yan Ta'addan da Suka Addabi Katsina

"Sai dai wani zazzafan bincike da aka yi a kan sa ya tabbatar da cewar shi din dan Obegu da ke karamar hukumar Onicha ta jihar Ebonyi ne kuma kwamandan tsagin Obegu ne."

Malamin addini ya bayyana yadda ya tsallake harin Boko Haram a masallacin Kano

A wani labarin kuma, mun ji cewa babban limamin Kano kuma shugaban jami'ar BUK, Farfesa Sani Zahradeen, ya bayyana cewar yana gab da tayar da ikamar sallar Juma'a ne lokacin da Boko Haram suka dana bam a masallacin da yake jagoranta a shekarar 2014.

Ya ce ya dunga jin ihun Allahu Akbar bayan ya tada kabbara daga nan ya ji karar fashewar abu sai kuma karar harbe-harbe suka biyo baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng