Yanzu Yanzu: Allah Ya Yiwa Jakadan Najeriya a Spain, Demola Seriki, Rasuwa
- Demola Seriki, jakadan Najeriya a kasar Spain ya kwanta dama a birnin Madrid a safiyar Alhamis, 15 ga watan Disamba
- Mummunan labarin na kunshe ne a wata sanarwa dauke da sa hannun yaran mamacin
- A watan janairun 2021 ne aka nada Seriki a matsayin jakada a kuma rike mukaman minista daban-daban a baya
Spain - Allah ya yiwa jakadan Najeriya a Spain, Demola Seriki rasuwa a ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba, jaridar Vanguard ta rahoto.
Marigayin ya mutu yana da shekaru 63 a duniya.
Labarin mutuwarsa na kunshe nea cikin wata sanarwa dauke da sa hannun 'ya'yansa, rahoton The Nation.
An kuma tattaro cewa tsohon ministan ya kwanta dama a cikin iyalinsa a ranar Alhamis.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sanarwar ta ce:
"Cike da nauyin zuciya da godiya ga Allah madaukakin sarki ne muke sanar da mutuwar miji, mahaifinmu, kakanmu, dan uwanmu, kawunmu kuma abokinmu."
Har zuwa mutuwarsa, shine jakadan Najeriya a Spain tun bayan da aka nada shi kan mukamin a watan Janairun 2021.
Ya taba rike mukamin karamin ministan harkokin cikin gida tsakanin 2009 zuwa 2010.
A watan Mayun 2009, sarkin Legas, mai martaba Oba Rilwa Akiolu, ya baiwa Demola Seriki sarauta a matsayin Otun Aare na Legas.
Ya kasance karamin ministan noma da albarkatun ruwa daga 2007 zuwa 2008.
Ya kasance minista mai kula da ma'adinai da ci gaban karafa daga Oktoban 2008 zuwa Disamban 2008.
Ya yi aiki a matsayin karamin ministan tsaro daga 2008 zuwa 2009.
Yar'uwar Mamman daura, Hajiya Laraba Dauda, ta kwanta dama
A wani labari makamancin wannan, mun kawo a baya cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa danginsa na Katsina ta'aziyyar babban rashi da suka yi na yar'uwarau, Hajiya Laraba Dauda.
Shugaba Buhari, a cikin wata sanarwa daga mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu, ya bayyana marigayiya Laraba wacce yaya ce Mamman Daura a matsayin mace mai kirki da jajircewa a kan yara da son yan uwanta.
Ya bayyana cewa yan uwa da dangi za su yi kewar marigayiyar wacce ta rasu ta bar 'ya'ya, jikoki da yan uwanta, inda ya roki Allah ya ji kanta da rahama..
Asali: Legit.ng