Budurwa ta Maka Tsohon Saurayinta a Kotu Kan Bashin N180,000 a Kaduna
- Budurwa ‘yar kasuwa mai suna Fatima Isma’il ta maka tsohon saurayinta mai suna Abubakar Shu’aibu a kotu kan bashin da take bin sa
- Fatima tace ta ranta masa kudi N230,000 ya gyara motarsa amma N50,000 kadai ya biyata kuma ya kalmashe ya ki biyan sauran
- Shu’aibu ya sanar da cewa bata ce bashi ta bashi ba kuma bashi da aikin yi don haka zai dinga biyan N20,000 duk karshen wata har ya gama biyanta
Kaduna - Wata budurwa ‘yar kasuwa mai suna Fatima Isma’il a ranar Laraba ta roki wata kotun shari’a dake zama a Rigasa Kaduna da ta umarci tsohon saurayinta, Abubakar Shuaibu da ya biya ta N180,000 da ta ara masa.
Daily Nigerian ta rahoto cewa, Isma’il ta sanar da kotun cewa ta bai wa Shuaibu bashin N230,000 don ya gyara motarsa kuma har yanzu N50,000 kadai ya biya ta.
Tace dukkan kokarin da tayi wurin karbar ragowar kudin daga tsohon saurayinta ya gagara.
A bangarensa, Shuaibu yace tsohuwar budurwarsa Fatima bata ce bashi ta bashi ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Bata son ganin damuwata. A duk lokacin da ta ga na damu, sai ta tambaye ni kuma ta bani kudi.”
- Yace.
Ya sanar da kotun cewa bashi da aikin yi.
Ya yi alkawarin biyan N20,000 a karshen kowanne wata har sai ya biyata kudinta dukkanshi, jaridar Vanguard ta rahoto hakan.
Alkalin kotun, Malam Abubakar Salihu Tureta ya bukaci wanda ake karan ya dinga biyan N30,000 Duk Wata farawa daga makon farko na watan Janairun 2023.
Budurwa ta karbo mota da ta ba saurayinta bayan shekaru 2 da rabuwarsu
A wani labari na daban, wata budurwa a bidiyon da ta fitar a TikTok ta bayyana yadda ta kwace motar da ta ba saurayinta bayan shekaru biyu da suka rabu.
Ta sanar da cewa da farko tayi masa hakyayyar karamci ne tayi biris da shi bayan sun rabu, amma daga bisani ta karbo.
Sai dai bakar kazantar da ta samu a cikin motar yasa sai da aka kwaseh awa uku ana aikin wanke motar kafin ta fito fes daga bisani.
Asali: Legit.ng