Rundunar Yan Sandan Nigeria ta Magantu Kan Samun Rubabbun Kudade Ta Bayyana mai Shi

Rundunar Yan Sandan Nigeria ta Magantu Kan Samun Rubabbun Kudade Ta Bayyana mai Shi

  • Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta mayar da martani ga wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta da ke nuna wasu rubbabbun kudi a Benue
  • Bidiyon da ake yadawa ya janyo cece-kuce a tsakanin 'yan Najeriya tare da nuna yatsa a tsakanin masu amfani da kafafen sadarwa na zamani
  • An gano wasu tsofaffin kuma rubbabun kudi da suka lalace a wani bidiyo da ya yadu shafukan sada zumunta

Benue: Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta karyata wani faifan bidiyo da ya nuna tarin wasu rubbabbun kudin da aka gano a wani shago da ke kusa da barikin ‘yan sanda a unguwar Wadata da ke garin Makurdi.

A cikin faifan bidiyon, ana iya ganin wasu ‘yan Najeriya suna fito da buhunan, wanda suke dauke da wasu takardu da ake ganin kamar rubbbaben kudi.

Kara karanta wannan

Katsina: ‘Yan Sanda Sun Ragargaji ‘Yan Bindiga, Sun Kama 2 tare da Ceto Mutum 5 da Suka Sace

Rundunar ‘yan sandan jihar Binuwai a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar SP Catherine Anene ta fitar a Makurdi, ta bayyana bidiyon a matsayin ‘Labarin da ba na gaskiya bane’.

Sai dai hukumar tayi alkawarin yin bincike, tare da gano sahihancin batun ko akasin haka kamar yadda kakakin ya sheda. Rahotan legit.ng

Rubabbun Kudi
Rundunar Yan Sandan Nigeria ta Magantu Kan Samun Rubabbun Kudade Ta Bayyana mai Shi Hoto: Prudence
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani bangaren sanarwar da kakin yan sandan yayi tace:

“A ranar 13 ga Disamba, 2022 da misalin karfe 12 na rana aka samu labarin a ofishin ‘yan sanda na Makurdi, cewa an gano wasu boyyeyyen kudi sanfurin Naira kusa da Barikin ‘yan sanda na Wadata".
“Jami’an ‘yan sanda da aka aika domin gudanar da bincike a wurin da lamarin ya faru, sun gano wasu bata gari a wani shago da ke kusa da Barikin ‘yan sanda na Wadata, Makurdi suna wasaso da wasu takardu wanda ba'a kai ga gano mainene ba"

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Da sanyin safiyar nan 'yan bindiga suka kone ofishin INEC a wata jiha, uku sun mutu

“An gayyaci mai shagon, Isah Suleiman domin yi masa tambayoyi, kuma ya ba da ba'asin shedar lasisin da babban bankin Najeriya, CBN ya ba shi na tattara tsoffin kudi.

Sanarwar ta kara da cewa, wadannan takardu da aka samu an same su ne daga CBN, kuma ana amfani da su wajen sarrafa maganin sauro. Kakakin yace zamu fadada binciken domin tabbatar da hakan.

Sabbin Kudin Da Babban Bankin kasa Ya Fito Dashi

Babban bankin Najeriya ya ba tabbacin cewa bankunan kasuwanci kasar nan sun shirya don samar da sabbin kudaden Naira daga gobe Alhamis 15 ga Disamba, 2022.

Kamfanin Jiragen Da Suke Jigilar Fasinjoji da Kaya a Nigeria Sun Sami Abokin Gabzawa a Kasuwancin

A wani labarin kuma, bayan samun amincewar gwamnatin tarayya, kwanan nan kamfanin Rano Air zai fara shawagi a sararin samaniyar Najeriya.

Kamfanin jirgin mallakin hamshakin dan kasuwa ne kuma hamshakin mai hada-hadar mai, Alhaji Auwalu Abdullahi Rano.

Don fara aikin jigilar, Rano ya kashe sama da Naira biliyan 4.2 wajen siyan sabbin jiragen.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida