Ma’aikatan Gwamnatin Filato Sun shiga Yajin Aikin Jan Kunne na kwanaki biyar

Ma’aikatan Gwamnatin Filato Sun shiga Yajin Aikin Jan Kunne na kwanaki biyar

  • Rashin samun albashi tsawon watanni uku ya tilastawa ma'aikatan gwamnati a jihar Filato tafiya yajin aiki
  • Ma'aikatan sun tafi yajin aikin jan kunne daga ranar Litinin inda za su kwashe kwanaki biyar babu aiki
  • Sun dauki wannan matakin ne bayan ganin take-taken gwamnatin jihar na yin kunnen uwar shegu da bukatunsu

Plateau - Ma'aikatan gwamnati a jihar Filato sun shiga yajin aikin jan kunne na kwanaki biyar wanda ya fara a ranar Litinin, 12 ga watan Disamba

Ma'aikata sun yanke shawarar daina aiki na wucin-gadi bayan gwamnatin ta ki biyansu albashi tsawon watanni uku, Premium Times ta rahoto.

Lalong
Ma’aikatan Gwamnatin Filato Sun shiga Yajin Aikin Jan Kunne na kwanaki biyar Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Dalilinsu na tafiya yajin aiki

Ma'aikatan sun kuma yanke shawarar tafiya yajin aiki saboda gazawar gwamnatin wajen sakin kudaden da ake ragewa kamar su kudaden fansho.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Kowa ya huta: Atiku ya fadi yadda zai yi kungiyar ASUU idan ya gaji Buhari a zaben 2023

A wani taron manema labarai da ya gudana a Labour House da ke Jos, babban birnin jihar Filato a ranar Litinin, shugaban kungiyar JNPSNC, Titus Malau, ya ce sun yanke shawarar shiga yajin aiki bayan ya fito karara cewa gwamnnatin bata yin abun da ya dace don biyansu albashin da suke bi.

Hukuncin ma'aikatan na shiga yajin aiki na zuwa ne kwana daya bayan shugaban ma'aikatan jihar, Sunday Chong, ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta biya su bashin albashin da suke bi.

Kungiyoyin kwadago sun aika wasika ga gwamnati kafin daukar wannan matakin

A ranar Alhamis da ya gabata, shugabancin kungiyoyin kwadagon daban-daban sun rubuta wasika zuwa ga gwamnatin jihar suna gargadin cewa ma'aikata za su shiga yajin aiki idan ba a biya albashin da suke bi ba a ranar Litinin.

Kungiyoyin sun ce wannan mataki ya zama dole saboda gazawar gwamnati wajen cika yarjejeniyar da suka cimmawa.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da Aka Tsinci Gawar Budurwa Cikin Wani Yanayi a Babban Birnin Jihar Arewa

Ya ce:

"Wannan ya zama dole duba da cewar gwamnatin ta gaza wajen cike bukatunmu kuma musamman yarjejeniyar da aka cimmawa a ranar 11 ga watan Nuwamban 2022, da sa bakin sakataren gwamnatin jihar.
"Bukatar JNPSNC sune kamar haka: Rashin biyan albashi na wata uku daga Satumban 2022 har zuwa yau; rashin sakin tsarin albashi; rashin sakin ragowar kudin fansho daga Agustan 2022 har zuwa yau da rashin sakin karin albashi na karin matsayi da karin kudi na shekara-shekara da sauransu."

Kungiyar ta kuma soki rahoton farar takarda na kwamitin da Nde Gobak ke jagoranta kan kin karawa ma'aikatan da suka kai girma, rahoton Daily Trust.

Shugaban kungiyar kwadago na jihar Plateau, Eugene Manji ya ce:

"Muna ta tsammanin za su cike yarjejeniyar a ranar ko kafin 14 ga watan Nuwamban 2022, sannan ya kamata a biya cikakken albashin watan Agusta sannan ya kamata a biya albashin Satumba/Oktoba kafin karshen Nuwamba amma ga shi muna a Disamba.

Kara karanta wannan

Bayan Kashe Ma'kudan Ku'da'de Wajen Gina Gada, Yanzu Dai Gadar Ta Fara Tsagewa

"Kai tsaye, gaba daya abun da muka tattauna da cimma matsaya a kai, babu abun da aka yi. Wannan na nufin basu mutunta yarjejeniyar tunda ko albashin Agustan rabi ne ya shiga. Don haka, muna iya fara kirgawa daga Agusta, Satumba, Oktoba, Nuwamba kuma a zahiri mun cancanci samun albashin Disamba a yanzu."

Atiku ya yi alkawarin ba matasa da mata aiki idan ya zama magajin Buhari

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya sha alwashin inganta rayuwar mata da matasa idan har aka zabe shi a matsayin wanda zai gaji Buhari.

Atiku ya ce musamman gwamnatinsa ta ware wasu makudan kudade don tallafawa mata da matasa a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng