Hotuna: Gwamna Sanwo-Olu Ya Zama Kuku, Ya Rangada Miyar Farfesu
- Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya nuna kwarewarsa a harkar girki a bikin dafa abinci na 2022 da aka yi a jihar
- Ga mamakin dubban mutane a wajen taron, gwamnan ya rangada miyar farfesun kifi
- A halin da ake ciki, akwai gasar dafa dafadukan shinkafa tsakanin manyan masu girke-girke na kasashen Kenya, Togo, Nigeria da Ghana
Lagos - Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya shiga sahun manyan masu girke-girke a bikin abinci na Legas na 2022.
A wajen taron, gwamnan na jihar Legas ya kuma shirya farfesun kifi domin jin dadin mutanen da suka halarci bikin, jaridar PM News ta rahoto.
Gwamnan ya yi girkin ne tare da Chef Gbolabo Adebakin da kuma shahararriyar mai girke-girke a Instagram “Diaryofakitchenlover” Chef Tolani.
Daya daga cikin shirye-shiryen bikin shine gasar girka dafadukan shinkafa tsakanin manyan kukun Kenya, Togo, Najeriya da Ghana.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ajiri daga kasar Ghana za ta yi karo da Chef Feyi na Najeriya, kamfanin dillancin labaran Najeriya ta rahoto.
Sanwo Olu ya yi jawabin godiya
Da yake jawabi ga taron, Sanwo-Olu ya bayyana cewa bikin wannan shekarar ya fi wadanda aka yi a baya, rahoton The Times.
Sanwo-Olu ya ce:
"Babban abun alfahari ne kasancewa na a nan da yammacin nan. Na jinjinawa dukkanin masu abincimu da suka fito suka shiga wannan biki.
"Ina godiya gareku ku duka kan kasancewa a bikin abinci na wannan shekarar kuma ina fatan cewa kowa zai samu abun komawa gida da shi.
"Wannan al'adarmu ce, wannan gadonmu ne, wannan shine abun da ya yi mu,, nan Lagas ne kuma muna alfahari da gadonmu.
"Muna alfahari da yadda muke mayar da abincinmu."
Miji nagari: Matar aure ta yi bidiyon mijinta yana tikar wanki
A wani labarin, wata matar aure ta garzaya shafukan soshiyal midiya domin nuna gamon katar da Allah ya yi mata na samun miji nagari mai sonta da hutu.
Matar ta wallafa bidiyon maigidan nata yana tikar wankin kayanta yayin da ita kuma take shakatawa a dandalin TikTok.
Matan aure da dama a dandalin sun tayata murna domin a cewarsu samun miji irin nata yana da matukar wahala a wannan zamanin.
Asali: Legit.ng