Buhari Ya Yi Alhinin Mutuwar Matar Tsohon Shugaban Hafsan Tsaro

Buhari Ya Yi Alhinin Mutuwar Matar Tsohon Shugaban Hafsan Tsaro

  • Allah ya yiwa Hajiya Binta Daggash, matar tsohon shugaban ma'aikatan tsaro, Air Marshall Al-Amin Daggash (mai ritaya) rasuwa
  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ta'aziyyarsa ga miji, yan uwa dangi da abokan huldar marigayiya Hajiya Binta
  • A sanarwar da Malam Garba Shehu ya fitar, shugaban kasar ya roki Allah ya ji kanta tare da ba yan uwanta hakurin rashin da suka yi

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ta'aziyyarsa ga tsohon shugaban ma'aikatan tsaro, Air Marshall Al-Amin Daggash (mai ritaya) kan mutuwar matarsa, Hajiya Binta Daggash.

Shugaban kasar a sakon ta'aziyyarsa zuwa ga tsohon shugaban sojin, iyalansa, gwamnati da mutanen jihar Borno ya yi addu'a kan Allah ya ji kanta, Daily Trust ta rahoto.

Buhari
Buhari Ya Yi Alhinin Mutuwar Matar Tsohon Shugaban Hafsan Tsaro Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Buhari ya bayyana marigayiyar a matsayin mai son jama'a

Kara karanta wannan

Mutuwa Mai Yankar Kauna: An Yi Babban Rashi A Ahlin Shugaban Kasa Buhari

Da yake jawabi a wani sako daga Malam Garba Shehu, kakakin shugaban kasa, Buhari ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A irin wannan lokaci na juyayi, kalaman baki ba za su isa komai ba. Za a dunga tunawa da ita kasancewarta mutum mai son jama'a, taimako da jajircewa."

Kakakin shugaban kasar ya ce marigayiyar wacce ta kasance malamar makaranta ta mutu ta bar mahaifiyarta, kanne bakwai, yara biyar da jikoki takwas.

Jawabin ya kara da cewa:

"Daga cikin yan uwanta akwai Malam Sule Umar, mai shirya fina-finai mazaunin Kano da Misis Aisha Umar Yusuf, matar mawallafin jaridar Daily Trust da kuma shugabar kungiyar labarai na Najeriya, Kabiru Yusuf.
"A matsayinta na tsohuwar shugaban matan ma'aikatan tsaro (DEFOWA), Hajiya Daggash ta yi iya bakin kokarinta wajen habaka ci gaba da ra'ayin iyalan jami'an rundunonin sojoji uku."

Shugaban kasar ya kuma yi addu'ar Allah ya ji kan marigayiyar, rahoton The Sun.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari: Da Gaske Aminu Ya Gana Da Shugaban Kasa? Gaskiya Ta Bayyana

Buhari ya yi alhinin mutuwar Hajiya Laraba Dauda, yayar Mamman Daura

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ta'aziyya ga danginsa na Daura kan babban rashi na yar'uwa da suka yi.

Hajiya Laraba Dauda wacce yar'uwa ce ga Mamman Daura ta a cikin makon nan inda ta bar 'ya'ya da jikoki.

A cikin sanarwar da kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu ya fitar, Buhari ya bayyana marigayiyar a matsayin mutum mai son dangi, inda ya roki Allah ya ba su hakuri da dangana kan rashinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng