Wanda Ya Fi Kowa Dadewa A Masallachin Harami Wajen Hidimtawa Ya Rasu Yana da Shekara 134
- Dattijun da ya shafe rayuwarsa kusan gaba dayanta a masallachin harami yana bautawa Allah safe da rana
- Tun Shekarar 1876 aka haifeshi kuma bayan da ya zama saurayi ya koma masallachin ko kuma ya tare gaba daya a can
- Wasu Na wa mukadimin alkunya da Barun haramin uban alakawari sabida yadda duk wanda yaje zai sameshi a wajen
Saudi Arabia: Sheikh Oudh Al Harbi ya kare rayuwarsa a masallacin Harami da ke Makah, kuma ana yi masa laqabi da "Kuruciya Mai Kyau" saboda tsayin daka da ya yi wajen yin Sallah a Masallacin Harami.
"Sheikh Awad Moawad Al-Subhi Al-Harbi,ya rasu yau a masallacin Harami" kamar yadda shafin Haramain ya wallafa a Twitter kuma kamar yadda Ummid.com suka hakkaito
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
'Alhazai na ganin sa akai-akai'
Sheikh Oudh Al Harbi ya zama yafi kowa zama da sallah a Masallacin Haramin Makkah, kuma ya kasance mai yawan yi dawafi.
Yawancin mahajjata ko alhazai da suke zuwa saudiya ko aikin Hajji da Umara na yawan ganinsa yana dawafi ko kuma yana sallah.
Makka ita ce Garin da aka haifi Annabi Muhammad (saw). Manzon Allah (SAW) ya rayu a Makka yana da shekaru 53. Daga baya ya yi hijira zuwa Madina inda ya rasu yana da shekaru 63 a duniya.
Annabi Muhammad (SAW) ya ce ladan yin Sallah daya a Masallacin Harami daidai yake da Sallah sau dubu dari (100,000). Wannan ya shafi duka biyun farilla (Farz) Sallah da na son rai (Nawwafil).
Wani Dalibi Ya Rasu Yana Sujjada
Dr. Muhammd Salah ya wallafa wani rubutu ya shafinsa na facebook yana mai bada wani labari na ban mamaki da kuma al'ajabi.
Ya fara da cewa wani dalibine dake karatu a jami'ar Al'azhar dake kasar misira ko kuma Egypt aka samu akan sallayyarsa yayi sujja kuma ya rasu.
Ya ce Yadda Abin ya faru shine lokacin da abokansa suka ga dan uwan nasu ya shafe kusan kwana uku basu ganshi a tsangayar koyar da aikin jinya da likitanci ba, tsangayar da yake karatu, sai suka je gidansa dan su duba.
Bayan sun je sai suka tarar da gidan a kulle duk hanayar da suka bi su bude sun gagara, sai suka sanar da jami'an tsaron 'yan sanda wanda kuma suka bude gidan da karfi kuma suka sameshi a akan sallayarsa yana sujjada kum aya rasu.
Tuni jami'an tsaro suka daukeshi zuwa asibitin jami'ar inda a nan ne aka tabbatar musu da cewa ya rasu.
Asali: Legit.ng