Kasar Afrika Ta Kudu Na Shirin Halasta Karuwanci Dukka Da Barazanar Yaduwar Cutar Kanjamau

Kasar Afrika Ta Kudu Na Shirin Halasta Karuwanci Dukka Da Barazanar Yaduwar Cutar Kanjamau

  • Ƙasar Afrika ta Kudu na shirin halasta karuwanci dukda matsalar yaɗuwar cutar kanjamau da ake samu a kasar wanda masana suka ce ta fi yaɗuwa ta hanayr kwanciya
  • Ƙudirine da aka kai gaban majalissar Ƙasar kan amincewarta ta bada damar halasta karuwancin da dangoginsa
  • Wata Ƙungiyar kare hakkin karuwai ce ta jagoranci kudirin ganin an amintar da halarcin a Ƙasar dan bawa masu sana’ar cikakken ƴanci

Ministan Shari'a na ƙasar ne ya kai dokar gaban majalissar ƙasar inda ya ke neman da ta sahale dokar karuwanci a fadin ƙasar.

BBC hausa ta rawaito cewa ministan na bukatar majalissar ne tayi duba game da dokokin baya da sukai magana akan karuwanci da na'uin su a fadin ƙasar

Dokar dai bata shafi halasta auren jinsi ba da kuma dokar hana safarar yara ko kuma yaran su shiga karuwanci ba.

Kara karanta wannan

Muna tare da CBN kan dokar kayyade cire kudi: Kungiyar Matasa

Ministan yace dokokin zasu taimaka wajen inganta rayuwar karuwai a ƙasar, kuma hakkan zai basu damar samun garkuwa daga wajen jami'an tsaron ƙasar wanda suka hada da na ƴan sanda da kuma na sa kai

ƙungiyoyi dai a ƙasar sun yi murna da wannan dokar, sannan sunce wani sabon babi ne na tabbatar da yanci a fadin ƙasar ta Afrika ta Kudu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Afrrika Ta Kudu
Kasar Afrika Ta Kudu Na Shirin Halasta Karuwanci Dukka Da Barazanar Yaduwar Cutar Kanjamau Hoto: Getty
Asali: Getty Images

Gwamnan Jihar Kogi ya Bada Dokar Rufe Gidan Karuwai

Gwamnann Jihar Kogi Yahaya Bello ya bada umarnin rufe gidan karuwai a jihar kogi.

Sannan gwamnann ya haramta sanya duk wani abu da kan iya rufe fuskar mutum a wajen taron jama'a wanda zai sa baza a ganeshi ba.

Bello ya bada umarnin ne na rushe wajajen ta hannun kwamishinan kula da ƙananan hukumomi da sarakuna, da masu kula da gine-gine na jihar.

Kara karanta wannan

2023: "Kun Yi Kaɗan" Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Ɗau Zafi, Ya Aike Da Kakkausan Sako Ga PDP

A ƙarƙashin sanarwar da bello ya bada ya kuma umarci ma;aikatar kula da gidaje da filaye a jihar kogi data rushe kangwayen da ba'a amfani da su ko kuma ba'asan na waye ba.

Wannan dai na kunnshe cikin shirin gwamnatin na tabbatar da tsaftace Kogi da kuma tabbatar da zaman lafiya mai nagarta a fadin jihar kaman yadda Yahaya Bello yake yawan fada a hirarrakin sa da manema labarai,

Asali: Legit.ng

Online view pixel