Kasar Afrika Ta Kudu Na Shirin Halasta Karuwanci Dukka Da Barazanar Yaduwar Cutar Kanjamau
- Ƙasar Afrika ta Kudu na shirin halasta karuwanci dukda matsalar yaɗuwar cutar kanjamau da ake samu a kasar wanda masana suka ce ta fi yaɗuwa ta hanayr kwanciya
- Ƙudirine da aka kai gaban majalissar Ƙasar kan amincewarta ta bada damar halasta karuwancin da dangoginsa
- Wata Ƙungiyar kare hakkin karuwai ce ta jagoranci kudirin ganin an amintar da halarcin a Ƙasar dan bawa masu sana’ar cikakken ƴanci
Ministan Shari'a na ƙasar ne ya kai dokar gaban majalissar ƙasar inda ya ke neman da ta sahale dokar karuwanci a fadin ƙasar.
BBC hausa ta rawaito cewa ministan na bukatar majalissar ne tayi duba game da dokokin baya da sukai magana akan karuwanci da na'uin su a fadin ƙasar
Dokar dai bata shafi halasta auren jinsi ba da kuma dokar hana safarar yara ko kuma yaran su shiga karuwanci ba.
Ministan yace dokokin zasu taimaka wajen inganta rayuwar karuwai a ƙasar, kuma hakkan zai basu damar samun garkuwa daga wajen jami'an tsaron ƙasar wanda suka hada da na ƴan sanda da kuma na sa kai
ƙungiyoyi dai a ƙasar sun yi murna da wannan dokar, sannan sunce wani sabon babi ne na tabbatar da yanci a fadin ƙasar ta Afrika ta Kudu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Jihar Kogi ya Bada Dokar Rufe Gidan Karuwai
Gwamnann Jihar Kogi Yahaya Bello ya bada umarnin rufe gidan karuwai a jihar kogi.
Sannan gwamnann ya haramta sanya duk wani abu da kan iya rufe fuskar mutum a wajen taron jama'a wanda zai sa baza a ganeshi ba.
Bello ya bada umarnin ne na rushe wajajen ta hannun kwamishinan kula da ƙananan hukumomi da sarakuna, da masu kula da gine-gine na jihar.
A ƙarƙashin sanarwar da bello ya bada ya kuma umarci ma;aikatar kula da gidaje da filaye a jihar kogi data rushe kangwayen da ba'a amfani da su ko kuma ba'asan na waye ba.
Wannan dai na kunnshe cikin shirin gwamnatin na tabbatar da tsaftace Kogi da kuma tabbatar da zaman lafiya mai nagarta a fadin jihar kaman yadda Yahaya Bello yake yawan fada a hirarrakin sa da manema labarai,
Asali: Legit.ng