An Kama Malamin Da Ya Zargi Shugaban Kungiyar Izala Da Sakataranta Kan 'Karbar Kudin 'Yan Siyasa
- Wani malami a Jihar Bauchi ya zargi malaman IZALA da mu’amala da 'yan siyasa da kuma rayuwar al’mubazzaranci
- A ranar Alhamis 1 ga watan Disambar wannan shekarar Sheik Kabiru Gombe ya magantu kan zargin da wani malami yai musu na mu’amala da ‘yan siyasa
- ‘Yan-Sanda Jihar Bauchi Sun cika hannu da wani malami kan zargin da yayiwa malaman 'kungiyar izalar, inda suka ce maganganunsa kan iya tada tarzoma
Bauchi: Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi sun tsare wani malamin addinin musulunci mazaunin garin Bauchi mai suna Abubakar Baba Karami bisa zarginsa da wasu kalamai kan 'kungiyar izala inda ya nuna malamanta suna mu’amala da ‘yan siyasa.
Malamin wanda aka fi sani da Afakhallah yayi wannan maganar ne akan mumbarin masallacin Juma’a a wani masallaci a jihar Bauchi a ranar 18 ga watan Nuwanban 2022.
Ya bayyanna sunan Kabir Muhammad Gombe da Abdullahi Bala Lau da Ahmed Sulaiman a matsayin masu ci da addini da kuma kar'bar ku'da’de a wajen 'dan takarar Shugaban Kasa na PDP Atiku Abubakar
Afakhallah yace malaman sunyi watsi da halayyarsu ta malanta tare da neman abin duniya da kuma biyewa 'kyale'kyalenta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Martanin Sheik Gombe Kan Batun
Lokacin da yake maida martini kan zargin da afakalla yayi masa, ya musanta zargin tare da tabbatarwa da afakallah cewa suna neman kudi kuma suna da kudi.
Sheik Gombe ya zargi Afakhallan da rashin sani tare da kuma tabbatar masa da cewa zai maka shi a kotu dan ya tabbatar da zargin da yayi musu.
“Muna zaman kanmu ba’a kasan kowa muke ba, kuma kaje Gombe ka tambaya; ina biyan sama da ma’aikata 200 a kasa na”
Matar Tinubu Tace Nan Gaba Za'ai Takarar Kirsita da Kirsita, Amma Yanzu Lokacin Muslmi Da Musulmi Ne
An Tsare Afakhallah
Lauyan wanda suke kara sun tabbatar da cewa anyi amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen batawa wa'dancan mutane suna tare da cin zarafin su.
“A cikin wa’azinsa ya kira malaman 'kungiyar izala da sunaye ir-iri wanda basu da da'din ji” kamar yadda ya zanta da jaridar WIKKITimes.
A cewarsa, lamarin ya dagula tare da 'daga hankalin mabiya 'kungiyar Izalar musamman ma a garin Bauchi, gudun haka yasa muka 'dau matakin doka sabida kar wanda abin ya shafa su 'dau mataki.
Kwamishinann 'Yan sandan jihar Bauchi ya umarci sashen binciken laifuka da ya binciki zargin da akeyiwa Afakhallah.
Jaridar WIKKITimes ta samu labarin cewa an gayyaci Afakallah ne a ranar 7 ga watan Disambar shekarar 2022 domin amsa tambayoyin da ake zarginsa akai.
A 'ko'karin da jaridar WIKKITimes tai na ji daga bakin Lauyan wanda ake zargi Barr Jibril Clinton abinda ya faskara
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi bai magantu kan wannan lamarin ba.
Asali: Legit.ng