Hajiya Laraba Dauda: Buhari Ya Yi Alhinin Mutuwar Yar’uwar Mamman Daura
- Allah ya yiwa yar’uwar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Laraba Dauda rasuwa a mahaifarsa da ke jihar Katsina
- Marigayiya Laraba wacce ta rasu ta bar yara da jikoki a doron kasa yar’uwa ce ga Mamman Daura
- Buhari ya mika ta'aziyyarsa ga yan uwansa inda ya bayyana marigayiyar a matsayin uwa mai kula da dangi
Katsina - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna alhini kan mutuwar yar'uwarsa, Hajiya Laraba Dauda.
Wata sanarwa daga fadar shugaban kasa ya bayyana cewa Hajiya Laraba ta rasu ta bar 'ya'ya da jikoki, jaridar PM News ta rahoto.
Yar'uwa ce ga Mamman Daura
Sanarwar wanda kakakin shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar a ranar Alhamis, 8 ga watan Disamba, ya ce Buhari ya mika ta'aziyyarsa ga ahlin nasa kan wannan rashi da suka yi na Laraba, wacce yaya ce a wajen Mamman Daura.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Shugaban kasar ya bayyana marigayiya Laraba a matsayin "uwa ba-da mama, mai cike da kuzari da wayi wacce ke kula da jin dadin yan uwanta.
Jaridar Leadership ta nakalto yana cewa:
"Mutuwarta abun bakin ciki ne amma Allah ya fi mu sanin abun da ya fi zama alkhairi. Ina mika ta'aziyyata ga duk wadanda ta bari a doron kasa.
"Allah Ubangiji ya ji kanta."
Yadda matashi ya zama lauya bayan ya rasa iyayensa da hannunsa daya tun yana karami
A wani labari na daban, jama'a sun taya wani matashi dan Najeriya murnar kammala karatunsa da kuma zama cikakken lauya duk da irin kalubalen da ya fuskanta a rayuwa.
Mahaifiyar Inyene Dominic Akpan ta rasu tun yana yaro dan shekaru 4 a duniya sannan mahaifinsa ya rasu yana da shekaru 5, hakazalika ya rasa hannunsa na dama a lokacin da yake shekaru 10 a duniya.
Duk da wadannan manyan kalubalen da ya fuskanta a rayuwarsa, Inyene be yanke kauna ba daga kudirinsa na son ganin ya zama cikakken lauya kuma mafarkinsa ya zama gaskiya da taimakon Allah, masoya, yan uwa da abokan arziki.
An rantsar da shi a matsayin cikakken Barista a ranar Talata, 6 ga watan Disamba a babban kotun koli ta kasar Najeriya.
Asali: Legit.ng