Babban Bankin Nigeria CBN Ya Sanar Da Sunan Mukaddashin Manajan Bankin NIRSAL

Babban Bankin Nigeria CBN Ya Sanar Da Sunan Mukaddashin Manajan Bankin NIRSAL

  • Biyo bayan sallamar da shugaba Muhammadu Buhari yayi tsohon manajan bankin NIRSAl, CBN ta sanar da wanda zai rike bankin
  • An sallami tsohon shugaban bankin NIRSAL bisa zargin cin hanci da rashawa da kuma kasa tafiyar da ofis
  • A farkon watan Nuwanban wannan shekarar aka kori shugaban bankin bada tallafin noma ga kananan manoman dan ingantashi

Abuja: Bayan tsige Manajan Darakta na Hukumar Rarraba Kayan Aikin Gona (NIRSAL) an nada sabon shugaban riko.

Saad Hamidu na Sashen Kudi na babban bankin Najeriya ne ya maye gurbin Aliyu Abdulhameed da aka kora a ranar Alhamis din da ta gabata bayan wasu korafe-korafe da ke kan cin hanci da rashawa.

NIRSAL
Babban Bankin Nigeria CBN Ya Sanar Da Sunan Mukaddashin Manajan Bankin NIRSAL Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kwafin takardar nadin Hamidu mai kwanan wata ranar 6 ga watan Disamba, 2023, wanda jaridar Daily Trust ta samu tace:

Kara karanta wannan

Buhari Ya Nemi Sahalewar Majalisa Kan Nada Mataimakan Gwamnan Babban Bankin CBN

“Ina farin cikin sanar da ku nadin Saad Hamidu a matsayin mukkaddashin manajan Hukumar Rarraba Kayan Aikin Noma ta Najeriya (NIRSAL) a yau"

Wasikar mai dauke da sa hannun Godwin Emefiele. Amma Hukumar daraktocin NIRSAL ta bayyana cewa nadin Hamidu na wucin gadi ne wanda zai shafe watanni uku ko wani abu makamancin hakan”

An Cire Tsohon Shugaban Bankin NIRSAL

Shugaba Muhammadu Buhari ya cire tsohon shugaban bankin NIRSAL Aliyu Abdulhamid bisa zargin cin hanci da rashawa da kuma kasa tafiyar da ofis.

A ranar daya ga watan Dsambar wannan shekarar aka sallami Aliyu Abdulhamid, sannan kuma aka sanar da kwamitin da zai gudanar da bincike kan zargin da akeyiwa tsohon shugaban manajan bankin.

Aiyukan bankin dai sun kara sanuwa ne ga 'yan Nigeria bayan kullen cutar korona wanda tasa abubuwa tashin gwaron zabi, da kuma yadda 'yan k'asa suka dukufa wajen yin noma da kiwo dan maye gurbin abinda suka rasa lokacin kullen cutar.

Zuwa Yanzu 'yan Nigeria na shakku kan shugaban nin hukumomin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari sabida yadda ake samunsu da cin hanci da rashawa. Alhalin kuma gwamnatin tai kaurin suna wajen yakar cin hancin

Asali: Legit.ng

Online view pixel