Likitoci Zasu Tafi Yajin Aikin Sai Mama Ta Gani A Jihar Abia
- A jihar Abia, likitoci sunyi barazanar shiga yajin aikin da ba ranar komawa har sai gwamnatin jihar ta biya musu hakkokinsu
- Likitoci a jihar Abia na bin gwamnati bashin albashin wata takwas gami da alawus-alawus, harma da na bashi
- Likitocin sun zargi gwamnatin jihar da maidasu bayi masu yi mata aiki ba tare da ko sisin kwabo ba
Abia: Kungiyar Likitoci ta Najeriya NMA ta bayyana cewa za ta fara yajin aikin sai mama-ta-gani a jihar Abia a ranar 8 ga watan Disamba, kan abinda gwamnatin jihar Abia ke yi mata.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban NMA, Dr Abali Isaiah, da Sakatarensa, Dokta Daniel Ekeleme, suka fitar, kuma tashar Channels Tv ta samu kwafin a ranar Laraba nan a Aba, babban birnin jihar .
Likitocin sun koka kan yadda abokan aikinsu da ke aiki a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Abia (ABSUTH) da Hukumar Kula da Lafiya ta Kasa (HMB) ke bin bashin albashi watanni 21 zuwa 25 da kuma watanni 13 na alawus.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake ke magana kan yadda likitocin ke fuskantar wahalhalu, shugaban NMA, ya zargi gwamnatin jihar da rashin nuna kwarewa wajen tafikar da hakar lafiya.
“Rashin biyan bukatun da aka ambata a sama, kafin ranar 8 ga watan Disamba, 2022 zai tilasta wa dukkan likitocin da ke aiki a karkashin gwamnatin tarayya, jihohi da kuma kamfanoni masu zaman kansu a jihar Abia su fara yajin aikin gaba daya,” in ji sanarwar.
"Ya kamata gwamnatin jihar Abia ta dauki alhakin duk wani halin tashin hanakali da kan iya faruwa a bangaren lafiya a lokacin da muka shiga yajin aikin". inji shugaban kungiyar
Shugaban ya kara da cewa:
"Kwananan aka baiwa gwamnatin jihar Abia rabu daga asusun gwamnatin tarayya dan biya tare da magance matsaltsalun albashi da bassussaka da ke addabar jihar."
Ga cikakken sanarwar da kungiyar NMA ta fitar a jihar Abia a kasa:
An fitar da sanarwar wannan ne a karshen taron gaggawa na kungiyar likitocin Najeriya (NMA) reshen jihar Abia da aka gudanar a gidan Farfesa Prosper Igboeli ( Sakatariyar Shiyyar NMA ta Aba) ranar Lahadi 4 ga Disamba, 2022 Abinda muka Lura:1. Cewa likitocin da ke aiki a ABSUTH da HMB suna bin bashin albashin watanni 21 zuwa 25 da kuma alawus na watanni 13.Bayani: mun bawa gwamnatin jihar Abia kwanaki 21 da ta biyan basussukan albashin da aka ambata, amma an ci kwana 17 bata ma kallemu ba.kuma kowa yana sane da yadda likitocin da ke aiki a ABSUTH da HMB suna fuskantar wahala da ba za a iya misaltata ba.Abinda muka cinma:Bayan bayanan abubuwan da aka ambata a sama, kungiyar NMA ta Jihar Abia ta yanke shawara kamar haka:1. Kungiyar NMA reshen jihar Abia ta yi Allah wadai da rashin biyan Likitocin mu dake ABSUTH da HMB.2. Har yanzu muna kan matsayar mu, kan cewa:3. Dole sai an biya kashi 50% na abin da muke bin su, kafin mu saurari bukatar gwamnati.4. Rashin biyan bukatun da aka ambata a sama ko kafin ranar 8 ga watan Disamba 2022 zai tilastawa dukkan Likitocin gwamnatin Tarayya, Jiha da wanda suke aiki a asibitoci masu zaman kansu a jihar Abia su shiga yajin yajin aikin gaba daya.Gwamnatin jihar Abia ta ɗauki alhakin duk wani abu da zai faru akan harkokin lafiya lokacin yajin aikinSa hannuDr Abali IshayaShugabaDr Daniel EkelemeSakatare. |
Asali: Legit.ng