Mina Cikin Mawuyacin Hali: Fasinjojin Jirgin Kasan Abj-Kd Suna Neman Daukin FG
- Fasinjojin da aka yi garkuwa dasu a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun fito neman tallafin gwamnatin tarayya
- Sun sanar da cewa suna cikin matsin rayuwa bayan samun ‘yancinsu saboda sun yi asarar kadarori tare da rasa ayyukansu
- Fasinjojin sun ce gwamnatin tarayya ta karba adireshinsu bayan fitowarsu amma har yanzu shiru, suna bukatar tallafi don fara sabuwar rayuwa
Wadanda farmakin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya ritsa dasu sun bukatar Gwamnatin tarayya da ta kawo musu dauki ta yadda zasu dawo rayuwarsu ta baya.
A watan Maris, gwamnatin ta dakatar da aikin jiragen kasa a hanyar Abuja zuwa Kaduna bayan farmakin da aka kai wa jirgin kasan.
Harin yayi sanadiyyar mutuwa da sace wasu fasinjoji. An sako fasinjojin daga bisani inda na karshe suka shaki iskar ‘yanci a watan Oktoba.
A ranar Litinin, karakainar jiragen kasan ta dawo a kan babbar hanyar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A yayin zantawa da manema labarai a ranar Litinin, wasu daga cikin fasinjojin sun ce ayyukan da suke yi sun subuce musu yayin da suke hannun ‘yan bindigan.
Malam Idris, daya daga cikin wadanda lamarin ya ritsa dashi, yace jami’an gwamnatin tarayya sun karba hanyar da zasu iya samunsu bayan sako su da aka yi amma tun daga nan shiru suke ji.
“A gaskiya sun karba adireshinmu kan cewa zasu neme mu. Amma har yanzu babu abinda suke ce mana.”
- Idris yace.
“Muna dai rayuwa ne cikin ikon Allah saboda a lokacin da aka sako mu, iyalanmu suna cikin wani hali, sun kuma sha gwagwarmaya. Batun gaskiya kenan.
“Da yawanmu mun siyar da kadarorinmu. A halin yanzu kowa yana fuskantar kalubale kan abubuwan da muka rasa. Da yawanmu ma’aikata ne yayi da aka kama mu, toh ba zasu jira har mu dawo ba.
“Da yawanmu mun rasa ayyukan yi da inda muke samun kudi. Muna ta kokarin fara sabuwar rayuwa ne.
“A matsayinmu na ‘yan kasa, wanda nake matukar alfahari da ita, ina tsammanin zasu kawo mana dauki.”
- Ya cigaba da cewa.
An sako ragowar fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna
A wani labari na daban, ragowar fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da ‘yan bindiga suka sace sun shaki iskar ‘yanci.
Shugaba Buhari ya gana da fasinjojin 23.
Asali: Legit.ng