Rana Ta Kwacewa Mai Bada Tsari Inda Ya Kashe Wanda Yaje Neman Maganin Bindiga
- Ana Yawan Samun Matsalar Gwajin Maganin Bindiga Musamman Ma Ga Masu Sai da Maganin
- Masu Fashi da makami, Garkuwa da Mutane na daga cikin na gaba-gaba wajen neman maganin bindiga
- Rike dai bindiga a Nigeria haramun ne muddin mutum bai samu sahalewar hukuma ba
Enugu: Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta cafke wani mai bada maganin gargajiya da kariya, bisa zargin kashe wani wanda yaje neman maganin bindiga wajensa
Mai Bada Maganin dan asalin jihar Enungun yana daga cikin mutane 17 da aka kama aka kuma akai holensu bisa zargin kisan kai, fashi da makami, kwacen manyan motoci, garkuwa da mutane, da kuma mallakar makami ba bisa ka’ida ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hakan ya fito ne a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Daniel Ndukwe, ya fitar a ranar Talata a shafin Twitter na rundunar.
Kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da, bindigu guda biyu, harsashi , bindigogin masu jigida guda uku, wata mota kirar Sino.
Sauran kayyyakin sun hada da buhunan siminti, wayoyin hannu, katunan ATM, da sauran abubuwa.
Yan Bindiga Sun Babbake Ofishin Yan Sanda, Jami'i Sun Rasa Rayukansu a Enugu
Wasu tsagerun 'yan bindiga sun kai farmaki Caji Ofis ɗin Inyi ɗake ƙaramar hukumar Oji-River, jihar Enugu, inda suka kashe 'yan sanda biyu a bakin aiki.
Maharan sun kuma cinna wa Ofishin wuta bayan tattara bindigu da Alburusai suka yi gaba da su a harin, wanda ya auku da safiyar ranar Lahadi a Ofishin yan sanda da ke Arum Inyi.
A wani bidiyo da wakilin jaridar Punch ya ci karo da shi ya nuna gawar mutum biyu da ake tsammanin 'yan sanda ne kwance a gaban harabar Ofishin.
Bidiyon ya nuna yadda Rufin Caji Ofis ɗin ke ci da wuta. Kazalika muryar dake magana a Bidiyon ta ayyana ɗaya daga cikin gawarwakin a matsayin ɗan sanda amma babu tabbaci game da ɗayan.
Asali: Legit.ng