Abu Mai Sosa Zuciya: Hotunan Wani Matashi Bai Ci Abinci Ba Tsawon Kwana 2 ya Samu Taimako
- Hotuna sun nuna yayin da wani dan Najeriya da ya suma akan hanya bayan kwana 2 bai ci abinci ba ya samu taimako daga wasu ma'aurata a Imo.
- Wasu ma'aurata a jihar Imo sun sha yabo a shafukan sada zumunta da muhawara kan yadda suka dauki nauyin wani mutum da ya suma a bakin hanya.
- Ma’auratan sun kai yaronsu makaranta, suka koma inda suka tarar da mutumin ya fada sumamme sabida bai ci abinci ba kwana biyu
Imo: Wata mata ‘yar Najeriya, Anoda Mirakle, ta ce ba da burinace ta mallaki duniya baki daya indai bata taimako ko kuma bazata cire mutane daga cikin halin kunci ba.
‘Yar wasan barkwanci wadda take zaune a Imo ta bayyana haka ne a shafinta na Facebook, inda ta bayyana yadda ita da mai gidanta suka kaiwa wani mutum wanda ya suma, su ganshi yahe a gefen hanya.
Yadda Abin Ya Faru
legit.ng tace: Ma'auratan sun kai yaronsu makaranta sai suka hangi mutumin a kwance akan titin cikin datti da kura.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sun sami labarin sunansa Akachukwu. Akachukwu ya shaida musu cewa bai san a inda yake ba saboda yunwar da yake fama da ita kuma yana da ciwon ulcer.
Akachukwu ya kara musu bayani da cewa:
“Ya ba da labarin cewa Oganshi ne ya kawo shi da wasu mutane daga Enugu a kan kwangilar aikin ginin otal a ph road, shi kuma (Oga) ya bar su a can tun kwana biyu babu kudin kashewa balle wanda zasu ci abinci."
"Yana da ciwon ulcer kuma ya kasa jurewa ciwon sai ya fara yawo domin neman aikin yini don samun 'yan kud'i da zai ci abinci. to shine ya suma a hanya ya fadi"
Kaddara Ta Riga Fata: Kyakkyawar Budurwa Ta Kaso Aurenta Bayan Watanni 3, Ta Wallafa Hotunan Shagalin Bikin, Jama’a Sun Yi Martani
Ma'auratan Imo sun samo masa maltina da madara sai wata mata da ke kusa da ita ta ba shi abinci.
Bugu da kari, sun ba shi kayan masarufi yayin da mutanen da ke wajen suka ba shi gudummawar N4k.
Ra'ayoyin Mutane a kafofin watsa Sadarwa
Nwogu Chiedobem MacDonald ya ce:
"Da kin taimaka masa ba tare da daukansa hoton ba, Allah ya saka miki da alkhairi."
Faith Chiamaka Hilary ta ce:
“Allah Ya saka muku da alheri, hakika mutaneda yawa sun wuce shi amma sai ku ne Allah ya taimaka kuka taimakeshi. Na gaya wa kaina, Dole ne in taimaki mutane (musamman batutuwan da suka shafi yunwa) akwai yunwa a ƙasar.
"Kai! Na gode da kuka zama na gari. "Allah ya saka muku da alheri."
Becky Chritz ya ce:
"Chai!!! Jama'a na fama da yawa a kasar nan oh...... Samun abincin da za su ci a kwanakin nan ya zama abin al'ajabi!"
"Kantin Tafi Da Gidanka": Bidiyon Wani Dan Najeriya Da Ya Mayar Da Baro Babban 'Kanti' Ya Birge Mutane Sosai
Wani Matashi Yana Dafa Abinci Yana Baiwa Babarata a Halin Yanzu,
A baya Legit.ng ta rahoto cewa wani matashi yana dafa abinci ya raba wa mabaratan akan titi.
Abin da ya fi daukar hankalin mutane ba wai kawai abinci ba ne, wanda ya bayar ya sanya kudi Naira 200 a kan kowane farantin abinci domin ya nuna ba wai kawai ya ciyar da su ba ne amma yana da sha’awar wadatasu.
Asali: Legit.ng