Tun Da An Samu Arzikin Man Fetur a Arewa, A Bari Mu Fita Daga Najeriya: IPOB

Tun Da An Samu Arzikin Man Fetur a Arewa, A Bari Mu Fita Daga Najeriya: IPOB

  • Kungiyar IPOB ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta bari yankin Igbo ya balle tun da Arewa ta sami mai
  • IPOB ta ce dama Arewa cima zaune ne kuma arzikin man yankin Igbo ne suke kwadayi suka hana kafa Biyafara
  • Gwagwarmayar kafa kasar Biyafara ya fara ne tun shekarar 1967 inda aka yi yakin basasa lokacin mulkin Yakubu Gowon

Kungiyar rajin kafa kasar Biyafara watau IPOB ta bayyana cewa tun da Arewa ta samu arzikin man fetur yanzu ya kamata a bari su balle daga Najeriya.

IPOB ta bayyana hakan ne ranar Juma'a a jawabin da ta fitar cewa ai tuni dama arzikin man feturin kudu da arewa ke amfana da shi yasa basu su son yankin Igbo su balle daga kasar.

Kakakin kungiyar, Emma Powerful, wanda ya fitar da jawabin yace yanzu Allah ya amsa addu'ansu Arewa ta samu mai, suna fatan hakan zai gamsar da gwamnati ta barsu su fita daga Najeriya, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Alkawari kaya: Tinubu ya fadi yadda zai yi da 'yan IPOB idan ya gaji Buhari a 2023

Zaku tuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya kaddamar da hakan arzikin man fetur karon farko a Arewacin Najeriya.

Kolmai
Tun Da An Samu Arzikin Man Fetur a Arewa, A Bari Mu Fita Daga Najeriya: IPOB Hoto: Presiddency
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

IPOB ta ce duk arzikin ma'adinan cikin kasa da Allah ya baiwa Arewa, yankin ya dogara kan arzikin man feturin yankin Igbo.

Yace:

"Arewacin Najeriya na da arzikin man fetur da ma'adinai. Amma saboda su cima zaune ne, shirya suke su yi duk mai yiwuwa saboda arzikin man kasar Biyafara."
"Yau, Allah ya daidaita matsalar duimbin shekaru tun da an samu mai a Arewa kuma hakan zai sulhunta gamayyar dole da aka kakabawa Najeriya.
Babu ruwan al'ummar Biyafara da man ku. Abinda muke bukata shine zaman lafiya don yin kasuwancinmu ba tare da yan ta'adda suna damunmu ba."
"Tun da kowa ya samu arzikin mai yanzu, shin za'a bari kowa ya kama gabansa?"

Kara karanta wannan

‘Yan Arewa Ku Shirya, Arziki na Kusanto mu Nan Babu Dadewa, Sheikh Gumi

Kamfanoni Sun Narka Hannun Jarin $3bn Bayan Gano Fetur a Arewa Inji Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da cewa fara hakan arzikin danyen mai da aka fara yi a Kolmani, iyakar jihohin Bauchi da Gombe ya kawowa Najeriya zubin jarin Dala biliyan 3.

Buhari ya bayyana cewa yan kasuwa daga kasashen waje ne suka zuba wadannan kudade.

Asali: Legit.ng

Online view pixel