Adadin Talakawan Dake jihohin Gombe, Yobe, Taraba, Bauchi, Borno, Adamawa: NBS
- Majalisar dinkin duniya UN ta yi ta'arifin talaka a matsayin wanda bai iya samun alal akalli $2 a rana.
- Kawo yammacin yau, ana sayar da Dalar Amurka $1 kudi N443.45 a kasuwar banki; Amma a kasuwar bayan fagge, ana sayar da Dalar Amurka a yau N780
- Hakan na nufin cewa duk wanda ai samun akalla N1500 a rana Talaka ne. Wannan na nufin abincin safe N500, na rana N500, na dare N500
Gwamnatin tarayya da hukumar kididdigar kasa NBS ta saki rahoton adadin mutanen dake cikin bakin talauci a kasar a shekarar 2022.
NBS a sabon rahoton da ta fitar ranar 17 ga Nuwamba ta bayyana cewa kashi 63 na dukkan ‘yan Najeriya suna cikin matsanancin talauci tare da fatara.
Kamar yadda binciken ya nuna, mutum miliyan 133 ne ke cikin bakin talauci na rashi abinci, kiwon lafiya, aikinyi, ilimi, dss.
A fadin kasa gaba daya, Jihar Sokoto ce ke da mafi yawan Talakawa.
Gwamnatin Buhari dai a bayan ta yi alkawarin fitar da yan Najeriya milyan 100 daga cikin kangin talauci.
A yankin Arewa maso gabas, jihar Bauchi ce tafi adadin masu fama da talauci, bisa jadawalin da TheCableIndex ta fitar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ga jerin adadin mutanen da cikin talauci a jihohin Arewa maso gabas:
Jiha | Adadin Talakawa | Alkaluma |
Gombe | Mutum Milyan 3 | 86.2% |
Yobe | Mutum Milyan 3.2 | 83.5% |
Taraba | Mutum Milyan 2.8 | 79.4% |
Bauchi | Mutum milyan 5.7m | 73.9% |
Borno | Mutum Milyan 2.3 | 72.5% |
Adamawa | Mutum 3.4m | 68.7% |
Bisa jadawalin, kashi 13.8% na al'ummar jihar Gombe ne kadai suke ci su koshi lafiya kulli yaumin.
Jihar Yobe kuwa, kashi 16.5% kacal ke samun cin abincin N500 da safe, N500 da rana, kuma N500 da dare.
A jihar Taraba, Bauchi da Borno, kashi 20% na dan dauri ne masu walwala.
Yan jihar Adamawa ne kadai suke da masu walwal da ya kai kashi 30%. Duk da haka, mutum biyu cikin ukun yan jihar Adamawa basu ci su koshi yadda ya kamata a rana.
Wannan Alkaluma na nuna cewa mafi akasarin al'ummar yankin Arewa maso gabas Talakawa ne.
Asali: Legit.ng