Kai Tsaye: Yadda Kamfen PDP Ke Gudana Yau A jihar Kwara

Kai Tsaye: Yadda Kamfen PDP Ke Gudana Yau A jihar Kwara

A yau Alhamis, 24 ga watan Nuwamba, 2022 jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP tana gudanar da taron yakin neman zabenta na shugaban kasa a jihar Kwara.

Tuni jiga-jigan jam'iyyar suka dira Ilori, babbar birnin jihar.

Atiku ya fara jawabi a taron

Atiku yace:

"Mun yi muku alkawarin samar da tsaro. APC lokacin da tazo ta yi muku alkawarin cewa zasu samar da tsaro cikin watanni shida da hawa mulki, amma me sukayi?
Bamu zo nan don yaudararku ba
Wahalar ta isa haka, shin zaku sake zaben APC, kuce a'a. Allah ya kiyaye
Al'ummar Kwara, ina son muku wata tambaya kuma ina son ku fada min gaskiya, shin ku nawa zaku zabi PDP?"
Saboda haka, al'ummar Kwara Allah muku albarka

Atiku, Ayu, sauran jiga-jigai sun dira Kwara

Dan takaran shugaban kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar, shugaban majalisar kamfe, Udom Emmanuel da sauran jigogin PDP sun dira Ilori.

Ya samu kyakkyawan tarba daga wajen tsohon gwamnan jihar Kwara AbdulFatah Ahmed, Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki dss.

Online view pixel