Dalilin da Yasa Aka Sauya Fasalin Takardun Naira, Shugaba Buhari

Dalilin da Yasa Aka Sauya Fasalin Takardun Naira, Shugaba Buhari

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa an inganta sabbin takardun Naira da wasu tsarikan tsaro ta yadda yin jabunsu zai yi matukar wuya
  • Ya bayyana cewa a kasar nan aka buga takardun kudin wanda hakan yasa yake matukar alfahari tare da yabawa sashen buga kudi na CBN
  • Shugaban kasan ya kara da cewa, ko a lokacin da Gwamnan CBN ya garzayo masa da bukatar sauya fasalin kudin, ya duba manyan dalilan ya gane cewa zasu amfani kasar

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba a Abuja ya kaddamar da sabbin fasalin Naira inda ya bayyana farin cikinsa kan sake fasalin kudin kasar nan da aka samar a cikin kasar karkashin Nigerian Security Printing and Minting (NSPM) PLC, Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bayan Buhari Ya Kaddamar, 'Yan Najeriya Sun Maida Martani Game da Sabon Sumfurin Kudin Naira

Buhari da Emefiele
Dalilin da Yasa Aka Sauya Fasalin Takardun Naira, Shugaba Buhari. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

A yayin jawabi yayin kaddamar da takardun kudin, wanda aka dasa kuma da taron majalisar zartarwa na tarayya, shugaban kasan yayin bayanin dalilin da yasa ya amincewa babban bankin Najeriya domin sake fasalin N200, N500 da N1,000.

Kamar yadda shugaban kasan yace:

“Sabbin takardun Nairan an yi su ne ta yadda zai yi wahala a yi jabunsu.”

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kara da cewa, sabbin takardun kudin zasu taimakawa Babban bankin Najeriya tare da tabbatar da sabbin manufofin kudi tare da assasa al’adun Najeriya.

Buhari ya yabawa Emefiele da tawagarsa

Shugaban kasa Muhammadu ya yabawa Gwamnan bankin, Godwin Emefiele da mataimakansa inda ya kara da godiya ga manajan darakta, zababbun daraktoci da ma’aikatan sashen buga kudi kan aiki tukuru da suka yi wurin tabbatar da sauyin takardun kudin cikin kankanin lokaci.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, Shugaba Buhari yace al’adar duniya ce sauya kudin kasa a duk shekaru 5 zuwa 8 amma yace Najeriya shekaru 20 kenan rabonta da ta canza kudi.

Kara karanta wannan

Mene ne Gaskiyar Lamarin? Bidiyon Sabbin Takardun Naira da Aka Canzawa Fasali Ya Bazu

“Wannan na nufin Naira ta dade da son sauya kamanni.
“Sake fasalin kudin kasa ana yin shi ne saboda wasu manufofi da suka hada da inganta tsaron kudin, kiyaye al’adarsu, kula da kudin dake yawo da rage tsadar kula da kudin.
“Kamar yadda aka sani, dokokinmu na gida, na Babban bankin Najeriya na 2007 ya bai wa babban bankin Najeriya damar fitarwa tare da sake fasalin Naira.
“Duba da wannan ikon, babban bankin ya zo wurina tun farkon wannan shekarar suna bukatar amincewa ta kan sauya fasalin kudin. Na duba dukkan dalilan da suka gabatar min.
“Akwai bukatar a gaggauta shawo kan matsalar yawan kudin dake yawo tare da wadanda ake boyewa ba a bankuna ba, rashin kudi masu kyau da yawaitar na jabu a manyan takardu. A saboda hakan ne na amince da sake fasalin N200, N500 da N1,000.”

- Shugaban kasan yace.

“Duk da hakan ba dole yayi wa wasu ‘yan Najeriya dadi ba, hudu daga cikin kasashen Afrika 54 na buga kudinsu a kasar su, Najeriya tana daya daga ciki.

Kara karanta wannan

Surkullen Tinubu a Bauchi: Zan ‘Sake Cajin Tafkin Chadi’ Idan na Zama Shugaban Kasa

“Don haka, da yawa cikin kasashen Afrika a ketare suke buga kudinsu kuma su shigo dashi kamar yadda muke shigo da kayayyaki.
“A Saboda haka cike da alfahari nake sanar muku cewa a Najeriya aka buga kudin nan a sashen buga kudi na Babban bankin Najeriya.”

- Yace.

Za a sauya fasalin Naira

A wani labari na daban, a ranar 26 ga watan Oktoba, Gwamnan babban bankin Najeriya ya sanar da cewa za a sauya fasalin Naira.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da hakan kuma za a fara fitar dasu a ranar 15 ga Disamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng