Daga Yanzu Za'a Rage Buga N500 da N1000, Zamu Fi Buga N20, N50, N100: CBN

Daga Yanzu Za'a Rage Buga N500 da N1000, Zamu Fi Buga N20, N50, N100: CBN

  • Babban bankin Najeriya ya bayyana cewa daga yanzu za'a fi buga kananan kudade don rage hauhawa
  • Gwamnan CBN, Mr Godwin Emefiele ya ce za'a rage yawan takardun N500 da N1,000 dake yawo
  • Ya bayyana cewa zasu fara kwafan kasashen da suka cigaba sosai inda manyan kudade ba su yawo

Babban bankin Najeriya CBN na shirin rage yawan takardun kudin N200, N500 da N1000 dake yawo cikn al'umma don rage hauhawan tattalin arziki.

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana hakan yayin zaman MPC na ranar 22 ga Nuwamba, 2022.

Sabbin kudi
Zamu Rage Buga N500 da N1000, zamu fi buga N20, N50, N100: CBN Hoto: @NigeriaGov
Asali: Facebook

Za'a fi buga kananan kudade

Shugaban na CBN ya bayyana hakan ne yayin hira da manema labarai kan matakan da ake dauka don tabbatar da rage kudaden boge da ake bugawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari Ya Kaddamar Da Sabon Kudin Najeriya

Emefiele ya ce ko a kasar Birtaniya, Fam 50 aka fi kashewa, sannan Fam 20, amma a Najeriya ba haka bane.

Ya ce adadin N500 da N1000 dake gari sun fi kananan yawa.

A cewarsa:

"Maganar gaskiya zamu rage adadin N200, N500 da N1000 da ake bugawa da wadanda ke yawo. Mutane su fara amfani da N50."

A cewar rahotanni, masu sharhi kan lamuran tattalin arziki sun bayyana cewa yan kasuwan da suka dogara kan kudin hannu wajen harka zasu ji jiki wannan karon.

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Bayyan Sabbin Takardun Kudin Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana sabbin takardun kudin Najeriya 'Naira' yau Laraba, 23 ga Nuwamba, 2023 a fadar shugaban kasa, Aso Rock Villa, Abuja.

Shugaban kasan ya bayyana kudaden ne a taron majalisar zartaswa FEC da ke gudana kowace Laraba.

Daga cikin wadanda suka halarci zaman akwai manyan jami'an fadar gwamnati, ministoci da gwamnan babban bankin Najeriya CBN.

Kara karanta wannan

Mene ne Gaskiyar Lamarin? Bidiyon Sabbin Takardun Naira da Aka Canzawa Fasali Ya Bazu

Hakazalika akwai shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC, Mr AbdulRasheed Bawa.

Dalilan sauya fasalin Naira uku, a cewar shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babu ja da baya game da lamarin sauya fasalin takardun kudin Najeriya 'Naira'.

Yace Tattalin arzikin Najeriya zai amfana da wannan abu saboda wadannan dalilai guda uku:

- Hauhawar farashin kaya zai ragu

- Masu hada kudaden jabu zasuyi asara

- Kudaden da yawo a gari zasu ragu

Asali: Legit.ng

Online view pixel