Yanzu-Yanzu: Mambobin Sun Tsige Kakakin Majalisar Dokokin Jiha Kwana 6 da Hawansa, Sun Nada Mace
- Yar majalisa mai wakiltan mazabar Emure a majalisar dokokin Ekiti, Olubunmi Adelugba ta zama sabuwar kakakin majalisa a jihar
- A ranar Litinin, 21 ga watan Nuwamba ne aka tsige tsohon kakakin majalisar jihar, Gboyega Aribisogan
- Aribisogan ya yi kwanaki shida ne kacal a kan kujerar kafin faruwar wannan sabon ci gaban
Ekiti - Yan majalisar dokokin Ekiti sun tsige kakakin majalisar jihar, Gboyega Aribisogan kasa da mako guda bayan zabansa, The Nation ta rahoto.
Mambobin majalisar 17 daga cikin 25 sun kada kuri'ar goyon bayan tsige Aribisogan daga kujerarsa. An kuma dakatar da shi har sai baba ta gani a ranar Litinin, 21 ga watan Nuwamba.
Sun kuma zabi Olubunmi Adelugba mai wakiltan mazabar Emure a matsayin sabuwar kakakin majalisar, rahoton Daily Trust.
Aribisogan ya zargi Kayode Fayemi da kitsa batun tsige shi
Arigbisogan ya zargi tsohon gwamnan jihar, Kayode Fayemi da kitsa wani makirci don a tsige shi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce Fayemi na hada kai da wasu yan majalisar dokokin guda bakwai din tsige shi a ranar Litinin.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja a gefen taron majalisar kakakin majalisun jihohi.
Ya ce:
"Nine sabon zababben kakakin majalisar dokokin jihar Ekiti. Na zo nan ne don yi maku jawabi kan rikicin da ya dabaibaye majalisar dokokin jihar Ekiti.
"Yan awanni da suka gabata, da misalin karfe 4:30 na asuba, wasu mambobinmu sun kira ni cewa yan majalisa bakwai cikin 25 na majalisar sun tafi tare da yan sandan Najeriya zuwa majalisar don shirin tsige ni ba bisa ka'ida ba domin su haifar da hargitsi a jihar Ekiti.
"Ina so nace a yanzu da nake magana, mambobin majalisar bakwai suna a zauren majalisar jihar.
"Mu biyu muka yi takarar kujerar na samu kuri'u 15, abokin hamayyata ya samu 10. Na yi nasara kuma aka rantsar dani a matsayin kakakin majalisa. Abubuwa na tafiya daidai cikin lumana kafin yan sanda su mamaye majalisar."
An nemi APC ta ceto damokradiyya a jihar Ekiti
Dan majalisar ya ce Ekiti na bukatar a ceto ta daga masu son rusa damokradiyya da zaman lafiya
Ya kara da cewar:
"Muna kira ga daukacin shugabannin APC a matakin jiha da kasa da su tashi sannan su ceto jihar Ekiti."
An zabi Aribisogan wanda ke wakiltan mazabar Ikole 1 a ranar 15 ga watan Nuwamba, a matsayin sabon kakakin majalisa.
Ya maye gurbin Funminiyi Afuye wanda ya rasu a ranar 1 ga watan Oktoba sanadiyar bugawar zuciya.
Awanni 24 bayan rantsar da shi, sai yan sanda suka mamaye zauren majalisar kan ikirarin cewa wasu na shirin kaiwa yan majalisar hari.
Asali: Legit.ng