Hatsarin mota ta yi sanadin rasa rayyuka 9 a Kano

Hatsarin mota ta yi sanadin rasa rayyuka 9 a Kano

- Mummunan hatsarin mota ya faru a kauyen Imawa da ke babbantitin Kano zuwa Zaria

- Hatsarin ya ritsa da trela, karamar mota da kuma adaidaita sahu inda mutum 9 suka rasu wasu suka jikkata

- Kwamandan hukumar FRSC na Kano, Zubairu Mato ya tabbatar da afkuwar hatsarin ya kuma ja hankalin matuka su rika kiyaye dokokin hanya

Mutum tara ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu uku suka jikkata sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru a Kano kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Hatsarin mota ta yi sanadin rasa rayyuka 9 a Kano
Hatsarin mota ta yi sanadin rasa rayyuka 9 a Kano. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Zubairu Mato, Kwamandan Hukumar Kiyayye Hadurra ta Kasa, FRSC, a jihar cikin wata sanarwa da ya ce hatsarin ya faru ne misalin karfe 9 na safe da ya ritsa da mota da adaidaita sahu a hanyar Kano zuwa Zaria a kauyen Imawa da ke karamar hukumar Kura.

DUBA WANNAN: FG ta bada umurnin sake tantance masu N-Power

Kwamandan ya ce hatsarin ya ritsa da trela mai lamba KMC158XW, wata karamar mota mai lama AE 884 GZW da adaidaita sahu mara lamba.

Ya ce trelan da motar sun yi karo ne a kokarin su na kaucewa adaidaita sahun da ke taho wa daga ta dayan bangaren titin.

Kwamdan ya ce cikin wadanda suka rasu akwai maza biyu, mata shida da yaro daya sai kuma wadanda suka jikkata su uku suna babban asibitin Kura da ke Kano.

KARANTA NAN: Yadda rundunar sojojin Najeriya za ta yi nasarar yaƙi da Boko Haram - Zulum

Ya bukaci masu ababen hawa su rika bin dokokin hanya domin kare afkuwar hadura.

A wani labarin daban, 'yan bindiga sun kashe jami'in hukumar yaki da masu fasakwabri wato kwastam yayin da ya ke bakin aikinsa a kauyen Dan Arau da ke babban titin Katsina/Jibya.

Sun kashe Garba Nasiru, mai mukamin mataimakin sufritanda ne yayin wani hari mai ban mamaki da suka kai a ranar Juma'a sannan suka tafi da bindigarsa AK 47.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel