Kwana 1 Da Yin Wa'azin Mutuwa Bayan Cikarsa Shekaru 40, Allah Ya Yiwa Wani Matashin Gombe Cikawa
- Allah ya yiwa wani matashi dan jihar Gombe rasuwa, kwana daya bayan wa'azin kusantar kabari
- Matashi ya yi murnar cikarsa shekaru 40 a duniya ranar Alhamis, 17 ga watan Nuwamba 2022
- Mutane da dama a shafinsa sun yi masa addu'ar Allah ya jikansa da rahama
Wani matashi mai binciken magunguna a littafan addinin Musulunci da tallansu kafar sada zumunta ta Facebook ya rigamu gidan gaskiya kwana daya bayan murnar cika shekaru 40 a duniya.
Matashin mai suna, Auwal Musa, mazaunin jihar Gombe ya yi wa'azin tunawa da ranar da zai mutu a shafinsa na Facebook a sakon cikarsa shekaru 40.
Kasa da awanni 10 da wannan jawabi a Facebook, Allah ya dauki ransa.
Wani daga cikin yan'uwansa yayi amfani da shafinsa ya sanar da labarin mutuwarsa.
Yace:
"Yan Uwa Mai wannan account din Allah ya karbi abinshi,muna naima kutayamuyi Masa addu'a,Ubangiji yasa yadace yasa ya huta,ameen,haka duniyan take ba komai bane."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gabanin mutuwarsa, Auwal Musa, ya bayyana cewa zagayowar ranar haihuwarsa na tuna masa mutuwa da shiga kabari.
Yace:
"17 ga Nuwamba jiya kenan (Alhamis), ranar da aka haifeni. Yanzu na cika 40. Alhamdulillah."
Kamar yanda na saba fada a irin wannan rana, hakika wannan kwanan wata na tinatar da ni kusantar #KABARI da Kuma dubi zuwaga rayuwata ayau da alakata da #UBANGIJI.
ISTIGFARI DA KANKAN DAKAI tare da BIN ALLAH da Kuma BIYAYYA WA IYAYE na da matukar muhimmanci a rayuwa.
Ya Allah Ka bamu ikon binKa tareda biyayya wa iyayen mu, Ka Karawa rayuwar mu albarka. Ka tsawaita rayuwar mu sannan Ka Kara Mata albarka."
Legit ta tuntubi wasu da suka san marigayin
Legit Hausa ta tuntubi wasu da suka san marigayin cikin har da wadanda suka halarci jana'izarsa.
Ahmad Muhammad Adamu ya bayyana mana cewa:
Allah sarki a gaskiya Iya sanin da na yiwa Malam Auwal mutum ne wanda yake son Addini sosai harma Yana yin Limanci wasu lokuta a masallacin Sarkin Kurba dake kufar gidansa a anguwar uku dake cikin garin Gombe kuma Yana daya daga cikin malaman Musabaka na kungiyar izala na Jos."
"Allah yasa yahuta."
Ibrahim Mahmoud wanda ya halarci jana'iza mamacin ya bayyana mana cewa:
Mutumin kirkine wlhy.. hafizi ne kuma he is friendly
Sunana Muhammad Yahaya (Baba-Yaro) daga fadan jihar Gombe ya laburta mana cewa;
Malam Auwal mutumin kirki ne mai son ganin mutane masu baiwa da fiƙira wato geniuses. Akan hakane ma yazo ɗaya daga cikin jagororin wata kungiyan matasa mai suna Arewa Genius Hub (AGH) reshen jihar Gombe. Sannan shine wanda ya bayyana wani dattijo mai baiwa a nan Gombe wanda ya ƙirƙiri murhun risho mai aiki da ruwa.
Malam Auwal mutum ne mai ilimin boko (kimiyya) da kuma ilimin addinin Islama.
Muna roƙo Allah ya gafarta masa. Allah yasa muyi kyakkyawan ƙarshe
Mutuwar wannan matashi ya girgiza jama'a
Mabiya shafin Matashin a Facebook da yan'uwan sun cika da addu'o'i ga mamacin.
Karanta jawabin mutane:
Auwal Abubakar yace:
"Allah ya Jikanshi da Rahma, Allah ya sa Yahuta, Allah ya bawa Iyalensa Hakurin Rashinsa, Allahumma Amin Summa Amin ya Hayyu ya Qayyum ya Zilzilali Wal'ikram"
Usman Buba Usman yace:
Innalillahi wa Innalillahirrajiun, Allah ya jikanshi da rahama, bansan wani aibunshi ba na dukkannin tsayon saninshi da nayi
Amy Raah:
Innalillaahi wa Inna ilaihi raaji'un
Allahumma gfirlahu allahumma thabbit hu
Zaliha Sani
Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun Allah ubangiji ya gafarta mishi yasa mutuwa tazam Hutu a gareshi damu Baki daya
Asali: Legit.ng