Tsohon Ministan Noma Tsaro, Shettima Mustapha Ya Rasu Yana Da Shekaru 83

Tsohon Ministan Noma Tsaro, Shettima Mustapha Ya Rasu Yana Da Shekaru 83

  • Babban bango ya fadi yayin da shahararren dan siyasa, Dr Shettima Mustapha, ya rasu yana da shekaru 83 a duniya
  • Mustapha ya rike mukamin ministan noma da al’barkatun kasa, ministan tsaro sannan daga bisani ya zama ministan harkokin cikin gida
  • Kungiyar manoman Najeriya ta bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi ga ma’aikatar noma dama kasar baki daya

AbujaTsohon ministan tsaro da noma, Dr Shettima Mustapha ya rasu a ranar Alhamis, 17 ga watan Nuwamba a babban birnin tarayya Abuja, jadaridar Daily Independent ta rahoto.

Tsohon hadiminsa a ma’aikatar tsaro wanda ya tabbatar da labarin mutuwar tasa, ya bayyana cewa za a dauki gawarsa zuwa garin Maiduguri, jihar Borno domin binne shi.

Marigayi Shettima
Tsohon Ministan Noma Tsaro, Shettima Mustapha Ya Rasu Yana Da Shekaru 83 Hoto: Independent
Asali: UGC

Hakazalika, wata sanarwa da shugaban kungiyar manoman Najeriya (AFAN), Arc. Kabir Ibrahim ya saki a ranar Alhamis, 17 ga watan Nuwamba ya ce mutuwarsa babban rashi ne ga kungiyar manoman.

Kara karanta wannan

Sauya Fasalin Naira: Miyetti Allah Ta Roki CBN Ya Kara Wa'adi Saboda Kada Fulani Suyi Hasara

Wani bangare na jawabin na cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Cike da rashi da tsananin radadi nake sanar da mutuwar mamba na kwamitin amintattunmu, Dr Shettima Mustafa, wanda ya faru yan mintuna kadan da suka gabata.
“A yanzu haka ana shirye-shiryen daukar gawarsa zuwa Maiduguri domin jana’izarsa bisa koyarwar addinin Musulunci.
“AFAN na kallon mutuwar daya daga cikin wadanda suka kafata a matsayin babban rashi.
“Har abada za a dunga tunawa tare da daraja sadaukarwar da ya yi a bangaren noma.
“AFAN na addu’an Allah ya ji kansa sannan ya baiwa iyalinsa juriyar wannan babban rashi da suka yi. Allah ya jikan, Dr Shettima Mustapha. Ameen.”

Takaitaccen tarihin marigayi Dr Shettima a siyasa

Dr Shettima Mustapha CFR ya kasance ministan noma daga 1990-1992 sannan a 2007 an nada shi a matsayin ministan tsaro a majalisar shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Na Zabi Shettima Musulmi Dan Uwana, Tinubu Ya Yiwa CAN Bayani

Daga bisani an nashi shi ministan harkokin cikin gida. Ya bar kujerar shugabanci a watan Maris 2010 lokacin da mukaddashin shugaban kasa Goodluck Jonathan ya rushe majalisar, rahoton Daily Post.

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya raba Mohammed Fadah da mukaminsa na Darakta Janar na hukumar NYSC a ranar Alhamis, 17 ga watan Nuwamba.

Sai dai zuwa yanzu babu wani dalili da aka bayar na cire shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng