Ngala: Zulum Ya Raba N255m, Kayan Abinci da Sutturu a Borno
- Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya rabawa jama’ar karamar hukumar Ngala tsabar kudi, kayan abinci da sutturu a ranakun karshen mako
- A cikin ranakun karshen makon nan Gwamna Zulum ya je har Ngala ya kwana biyu domin kaddamar da ayyukan tallafi
- Yankuna uku na Ngala suna cikin inda ambaliyar ruwa yafi ratsawa a jihar wanda yasa manoma suka tafka mummunar asarar
Borno - Daga cikin ayyukan jin kai na kwanaki biyu da ake ti a karamar hukumar Ngala ta jihar Borno, Gwamna Babagana Umara Zulum a cikin kwanakin karshen mako ya raba kayan Abinci na N255 miliyan tare da tufafi ga mutum 70,000 masu Karamin karfi kuma mazauna yankin.
Wannan tallafin an yi shi ne a wuraren da suka hada da: Garin Ngala, Gamboru da Wulgo duk a karamar hukumar Ngala wanda mata da maza duk sun samu kayan, jaridar The Nation ta rahoto.
Zulum ya isa Gamboru a ranar Juma’a inda yayi kwanaki biyu yana lura da ayyukan jin kai tare da wasu ayyukan cigaba.
“Da yawa daga cikin yankunan Ngala sun fuskanci tsananin ambaliyar ruwa wanda ya hana da yawansu zuwa gonakinsu. Saboda haka muka bayar da tallafi kuma zamu cigaba da taimakon jama’a da suke bukata har sai sun iya tsayuwa da kafafunsu.”
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
- Zulum yace.
Zulum ya Bude Kasuwar Shanu ta Gamboru Ngala
Kafin raba kayan abincin a ranar Lahadi tare da kudi da sutturu, Gwamna Zulum a ranar Asabar ya sake bude babbar kasuwar shanu ta Gamboru wacce aka rufe sama da shekaru bakwai sakamakon al’amuran ‘yan Boko Haram.
Bayan bude kasuwar, manyan tireloli Dankare da shanu sun bar Gamboru daga Maiduguri zuwa wasu sassan Najeriya.
A yayin bude kasuwar, Zulum ya ja kunnen ‘yan kasuwar kan zagon kasa ga tsaro wanda yace gwamnatinsa ba za ta taba lamunta ba.
Ba wannan bane karon farko da Zulum ke bada tallafi ba
Wannan ba shine karo na farko da Gwamna Zulum ya fara gwangwaje jama’ar Borno da tallafi tare da kayan jin kai ba.
Hatta ‘yan gudun hijira dake sansani ko zasu koma gida suna samun tallafin makuden kudi, kayan abinci da sutturu.
Asali: Legit.ng