Wani Mai Garkuwa Da Mutane Ya Bayyana Yadda Yake Kashe Naira Miliyan Daya Kullum Akan Karuwai

Wani Mai Garkuwa Da Mutane Ya Bayyana Yadda Yake Kashe Naira Miliyan Daya Kullum Akan Karuwai

  • Satar Mutane dai dan karbar kudin fansa na kara ta'azzara a Nigeria Musamman ma yankunan arewa maso yamman kasar
  • Ko a kwannan ma dai hukumar Tsaro sojojin kasar ta fitar sanarwar kashe kasurgumin main fashin dajin nan wato Dogo Mamman
  • Masu satar mutane na sanyawa 'yan uwan wanda sukai garkuwa dashi kudade masu yawa dan karbar fansar sa.

Rivers: Jami’an hukumar amsa bayanan sirri na hukumar ‘yan sandan Najeriya (FIB-IRT) sunyi awon gaba da wasu da ake zargin masu satar mutane ne da suka sace matar wani fitaccen dan kasuwa a jihar Rivers, watanni takwas da suka gabata.

Matar mai suna Mrs Hussana Adamu, tana kan hanyarta ne na ajiye ‘ya’yanta a makaranta lokacin da masu garkuwa da mutane suka dirar mata da muggan makamai sukai gaba da ita.

Kara karanta wannan

Soyayya Ruwan Zuma, Yadda Wata Budurwa Ta Fada Tekun Lagas Akan Saurayi

Yan Sanda
Wani Mai Garkuwa Da Mutane Ya Bayyana Yadda Yake Kashe Naira Miliyan Daya Kullum Akan Karuwai Hoto: Thisday
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake zantawa da manema labarai Mai Magna da yawun yan sanda jihar yace

Tawagar DCP Tunji Disu, ta kama hudu daga cikin wadanda ake zargin: Isiaka Hamidu, mai shekaru 30, wanda ya fito daga jihar Adamawa; Nwasaneo Goodluck , 34 ; Victor Nwidee, 29

Babban wanda ake zargin Isiaka Hamidu wanda ke sana'ar sai da AKu da Dawisu a Fatakwal, ya bayyanawa 'yan sandan yadda ya gayyaci wasu masu garkuwa da mutanen don su yi awon gaba da Mrs Adamu.

Kafin ya gayyace su, ya ce ya dauki wasu kwanaki yana samun bayanan da suka dace game da ita, musamman ma yadda take zirga-zirga

Ya kuma kara da cewa ya yi garkuwa da matar ne domin ramuwar gayya da laifin da mijinta Musa Ahmad ya yi wa kaninsa, wanda dan asalin garin Maiduguri ne a jihar Borno, amma kuma mazaunin garin Fatakwal na jihar Ribas ne.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wasu Fitattun Malamai Biyu a Jihar Arewa

Ya Abun Yake

A cewar wanda ake zargin kamr yadda jaridar Vanguard ta rawaito yace

Daya daga cikin ‘yan uwana ya yi aiki da Alhaji Musa Ahmad, tsawon shekara 11. Lokacin da ya tashi aure, iya abin da Alhaji Ahmad zai iya bashi shi ne Naira 250,000.
Ban yi farin ciki da hakan ba domin kowa ya san cewa yana da arziki sosai kuma zai iya biyan fiye da haka. Na yanke shawarar sace shi ko duk wani danginsa
Na tuntubi Goodluck, abokina na fada masa halin da ake ciki. Shima ya fusata sannan yai na'am da ra'ayina.
Nai Sa’a kwa ya kira shugaban kungiyar, Ojukwu, wanda ya shirya garkuwa da matar, bayan na nuna musu gidanta. Amma ban bisu ba sabida kar wani ya gane ni”.

Ya ce ya samu Naira miliyan 1.3 a matsayin kason sa na kudin fansa. Da aka tambaye shi me ya yi amfani da kudin, sai ya ce:

Kara karanta wannan

Rikicin Makiyaya da Manoma Ya Barke, An Yi wa Kauyuka 10 Kaca-kaca a Jihar Kano

Na yi amfani da Naira miliyan 1 ne wajen yin lalata da mata masu zaman kansu
INa kwana da Matan Bariki akalla biyu a kowane dare tsawon wata daya kuma na biya su Naira 20,000 kowacce.
Na yi amfani da ragowar Naira 300,000 wajen shuka masara a kauye,” in ji shi, yana mai cewa wannan ne karon farko da ya fara yin garkuwa da mutane.

A nasa bangaren, Goodluck, Yayi babbar difloma daga kwalejin Fasa Ta jihar Abia, ya amince da karbar Naira miliyan 5.5 daga hannun shugaban kungiyar bayan da aka biyasu kudin fansa.

Ya ce, “A cikinta na ciro Naira miliyan biyu, na ba Isiaka Naira miliyan 1.3 yayin da Victor ya samu N500,000.

Wani wanda ake zargi, mai suna ThankGod, ya ce bai da masaniyar cewa mambobin kungiyar na yin garkuwa da mutane.

Ya ce an tuntube shi ne domin ya yi amfani da motarsa ​​ya kai su wani wuri a karamar hukumar Bori Khana da ke jihar, bayan sacematar

Kara karanta wannan

Rikicin APC: 'Yan Daba Sun Kaiwa Ayarin Ado Doguwa Hari a Kano, Ya Magantu Kan Masu Hannu

“Shugaban kungiyar ya ce

In kai shi wani wuri a cikin motata. A hanya na dauko wasu abokansa guda uku. Daga nan ne ya kai ni kusa da gidan wanda akai yi garkuwa da ita wato maboyarsu . A lokacin ne na san su masu garkuwa da mutane ne”

Wanda ake zargi na hudu, Victor, ya bayyana cewa aikinsa shi ne kula da motsin wandawanda sukai garkuwa da su da kuma neman wasu hanyoyi da wanda suke tare zasu ringa yin zirga-zirga

Ya kuma tabbatar cewa ya karbi Naira 500,000 daga hannun Goodluck, a matsayin kasonsa na kudin fansa, inda ya bayyana cewa ya yi amfani da kudin ne wajen gyara motarsa ​​kirar Toyota Corolla.

A halin da ake ciki, rundunar ‘yan sandan ta ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa, wanda ake zargin shugaban kungiyar, Ojukwu, shi ne shugaban wata kungiyar asiri da aka fi sani da Dem-Bam a yankin Khann, wanda ke cikin jerin sunayen da ake nema ruwa a jallo.

An gano wata karamar bas, Toyota Avensis mai bakin gilashi da kuma mota kirar Toyota Corolla daya daga hannun wadanda ake zargin.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida