Mutane Na Cigaba da Fito da Kudin da Suka Boye, An Gano N200 da Aka Buga Tun 2003

Mutane Na Cigaba da Fito da Kudin da Suka Boye, An Gano N200 da Aka Buga Tun 2003

  • Masu kudin da suka boye su na tsawon shekaru suna dawo da su banki a dalilin wa’adin da Gwamnan CBN ya bada
  • Ana zargin kudi sun fara dawowa asusun bankuna ne domin a iya maidawa CBN kafin a fara buga sababbin Nairori
  • Amma wasu ma’aikatan banki sun shaida mana ana zuzuta maganar yadda mutane ke maida kudi zuwa akawun

Nigeria - Wasu mutanen Najeriya suna ta yunkurin tsallake wa’adin da gwamnan babban banki na CBN ya bada na dawo da tsofaffin kudi.

Legit.ng ta kawo labari an ga wasu tsofaffin kudi da ake zargin an boye su ne wanda yanzu bidiyonsu ya bayyana a shafukan sada zumunta.

A wannan bidiyo za a iya ganin takardun kudin N200 da aka buga tun shekarar 2003, kimanin shekaru 19 da suka wuce kenan da fitar da su.

Kara karanta wannan

An Tafka Mummunan Ta'asa Yayin da Sojoji Suka Dakile Kazamin Harin Yan Ta'adda a Jihar Arewa

Wannan sabon fai-fan bidiyo ya nuna wata ma’aikaciyar banki tana daukar hoton kudin yayin da ake jera su kamar yadda CBN ya buga su.

Za a ji muryar ma’aikaciyar tana mai zargin cewa an boye kudin ba tare da an kashe su ba.

A cewar ta, wadanda suka kawo takardun kudin banki sun yi haka ne domin a iya maida su cikin asusun gwamnati kafin lokaci ya kure.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsofaffin N200
Tsofaffin N200 Hoto: Getty Images da WestEnd61
Asali: Getty Images

Rahoton yace wasu masana suna tunanin cewa fito da kudin da ake yi shi ne ya jawo darajar Naira take karyewa a kasuwa a kwanakin nan.

Kudi ba su shigowa bankuna yadda ake tunani

Legit.ng Hausa tayi magana da wani ma’aikacin wani banki a garin Zaria, wanda ya shaida mana mutane ba su faye shigar da kudi a asusunsu ba.

Wannan ya nuna akwai yiwuwar masu kudi da-dama sun karkata ne wajen sayen kadarori da hatsi wanda hakan ya kawo tashin farashi a kasuwa.

Kara karanta wannan

Rikicin Makiyaya da Manoma Ya Barke, An Yi wa Kauyuka 10 Kaca-kaca a Jihar Kano

A cewar wani ma’ikacin bankin musulunci a garin Abuja, yanzu kudi suna shigowa banki fiye da yadda aka saba, amma ba a yadda ake rayawa ba.

Kamar yadda ya shaida mana ba tare da bari a kama sunansa ba, abin bai kai yadda ake tunani ba, ana sa ran sai karshen Nuwamba abin zai karu.

Za a fito da 'yan gidan yari

An ji labari Ministan harkokin cikin gida na kasa, Rauf Aregbesola zai zauna da Kungiyar NGF domin ganin yadda ‘yan gidan yari za su rage yawa.

A gidajen yari 253 da ake da su a Najeriya, ana tsare da mutum fiye da 75, 600, Aregbesola yana ganin wadanda ake garkame da su sun yi yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng