Wani Sanata Daga Yankin Kudu Maso Gabashin Nigeria Ya shigar Da Buhari Kara

Wani Sanata Daga Yankin Kudu Maso Gabashin Nigeria Ya shigar Da Buhari Kara

  • Sanata Ifeanyi Ararume Ya bukaci kotu Da ta tantance ko shugaba Kasa muhammad buhari yana Hurumin Tsige shi a matsayin shugaban kamfanin mai na kasa NNPC
  • Dan siyasar haifaffen Imo kuma yana neman N100bn a matsayin diyyar diyyar da aka tsige shi.
  • Ararume ya shigar da kara mai lamba FHC/ABJ/CS/691/2022 akan shugaba Buhari a ranar Laraba.

Birnin Tarayya - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gurfana a gaban wata babbar kotun tarayya dake Abuja bisa zargin tsige Sanata Ifeanyi Ararume a matsayin shugaban rikon kwarya na kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) da aka kafa.

Jaridar NewTelegraph ta rawaito cewa "a ranar Laraba, 9 ga watan Nuwamba, Ararume, ya caccaki gwamnatin tarayya da Buhari ke jagoranta, ya kuma nemi kotu tasa a biya shi diyyar naira biliyan 100.

Kara karanta wannan

Atiku Yana Da Tambayoyi Da Zai Amsa Kan Alakarsa Da Yan Ta'adda, In Ji Fani-Kayode

Shugaba Muhammadu Buhari 
Hoto: Legit..ng
Wani Sanata Daga Yankin Kudu Maso Gabashin Nigeria Ya shigar Da Buhari Kara
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Me yasa Sanatan Ibo ke kai Buhari kotu?

Ararume ya yi ikirarin cewa N100bn itace diyyar za'a biya shi bisaa cire shi ba bisa ka'ida ba.

Sanatan ya yi ikirarin cewa an cire shi ne a matsayin shugaban NNPC bayan an yi amfani da sunansa wajen Kaddamar da Kamfanin.

Lauyoyin da suka wakilci ararume dai suna hada da Cif Chris Uche (SAN), Ahmed Raji (SAN), Mahmud Magaji (SAN), Ogwu James Onoja (SAN), K.C Nwufor (SAN) da kuma Gordy Uche (SAN) tkamar yadda aka gani a wata takarda mai dauke da FHC/ABJ/CS/691/ 2022 a madadin Ararume.

Halin Da ake ciki Tsakanin Buhari da Ararume

Ararume ya bukaci kotu ta duba batutuwa guda 4: ciki kuwa har da batun ko ikirarin da yayi na cewa

kotu ta fassara sashe na 63(3) na dokar masana’antar man fetur ta shekarar 2021 kan ko shugaban kasa yana da hakki na tsige shi daga mukaminsa na shugaban NNPC ba bisa ka’ida ba.

Kara karanta wannan

Dattawan Yarbawa Sun Tsaida 'Dan Takaransu Tsakanin Tinubu, Atiku, Obi da Kwankwaso

Yadda Range Rover, N40m ya kai shugaban EFCC Abdurasheed Bawa a gidan yarin Kuje

A baya Legit.ng ta rahoto cewa an yankewa Abdulrasheed Bawa, shugaban EFCC hukunci tare da tsare shi a gidan gyaran hali na Kuje.

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ya ki yin biyayya ga hukuncin da kotu ta yanke wanda ya bayar da umarnin a saki wata mota kirar Range Rover wanda kudinta ya kai naira N40m ga wani Rufus Adeniyi Ojuawo, wanda aka sallame shi kuma aka wanke shi a shekarar 2018 daga zargin karbar cin hanci.

Mai shari’a Chizoba Oji na babbar kotun tarayya da ke Maitama Abuja ya umarci sufeto janar na ‘yan sanda Usman Alkali-Baba, da ya aiwatar da umarnin kotu kan Bawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida