Duniyar Kannywood Ta Shiga Yakin Neman Zaben Tinubu/Shettima
- Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya fadada kwamitin yakin neman zaben kujerar shugaban kasa a 2023
- Bayan tsame sunayen wasu yan Kannywood, Tinubu ya bada umurnin zuba yan wasan kwaikwayon tafiyarsa
- A watan Oktoba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyarar kwana biyu jihar Kano
Jos - Dirakta Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasan jam'iyyar APC, Gwamna Simon Lalong, ya amince da shigar da yan wasan kwaikwayon Hausa Kannywood cikin kwamitin.
Lalong ya sanar da hakan a jawabin da mai magana da yawunsa, Dr Makut Macham, ya fitar ranar Talata a Jos.
Yace an shigar da jaruman ne saboda tabbatar da an dama da yan wasan kwaikwayo da nishadi daga yankin Arewa cikin harkar kamfe.
Lalong ya ce sun yanke shawaran haka ne biyo bayan ziyarar da dan takaran APC, Bola Tinubu, ya kai jihar Kano inda ya gana da jaruman na Kannywood.
Yace Tinubu a Kano ya yi musu wannan alkawari.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya yi kira garesu suyi amfani da son da jama'a ke musu wajen janyo hankalin mutane don su zabi Tinubu da Shettima.
A cewar jawabin, jagoran wannan kungiyar ta yan Kannywood shine Abdu;-Mahmud; Ismail Afakalla mataimakin dirakta, da kuma Sani Muazu matsayin sakatare.
Yan wasan da suka tarbi sun hada da Ali Nuhu, Maryam Yahaya, Hadiza Kabara, Dan Dolo, Dan Gwari, da sauran su.
An Nemi Tinubu an rasa wajen muhawara
A karshen makon da ya gabata ne tashar AriseNews tare da hadin kan cibiyar cigaban demokradiyya CDD sun shirya taron tattaunawa tsakanin yan takara kujeran shugaban kasa.
Wadanda suka jagoranci shirin sun bayyana cewa an gayyaci yan takaran jam'iyyar APC, PDP, NNPP, LP, da PRP.
Yayinda dan takaran PDP, Atiku Abubakar, ya samu wakilcin mataimakinsa Ifeanyi Okowa; an nemi Tinubu ko wakilinsa an rasa a zaman.
Wannan ya haifar da cece-kuce inda aka fara rade-radin cewa shi tsoron me Tinubu ke ji bai iya fuskantar jama'a.
Sakamakon haka kwamitin kamfen jam'iyyar LP tace dan takararta ba zai sake halartan wani muhawara daTinubu da Atiku ba zasu halarta ba.
Dan takaran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, kuwa bai fadi komai game da hakan ba.
Asali: Legit.ng