Za'a Maida Kiristocin Nigeria Saniyar Ware a Karkashen Takarar Musulmi da Musulmi

Za'a Maida Kiristocin Nigeria Saniyar Ware a Karkashen Takarar Musulmi da Musulmi

  • Har yanzu dai ana samun maganganu tsakanin mabiya addinai a Nigeria, kan takarar Tinubu da Shettima
  • Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir Lawal da tsohon kakin Majalissar Dokokin Kasa Na gaba-gaban wajen sukar wannan tsarin
  • Simon Lalong Gwamnan Jihar Pleatue ne dai Babban Daraktan yakin zaben Jam'iyyar APC mai mulki

Shugaba kungiyar dattawa mabiya addinin kirista na arewa, Oyinehi Ejoga, ya yayi kira da mabiya addinin kirista da kar su marawa jam'iyyar APC baya sabida yadda sukai shakulatin bangaro da su.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai a taron kolin Zauren, rahoton Punch.

Yace maimakon ace jam'iyar APC ta yi yadda ake yi na bin tsari, amma ta yi watsi da hakan inda ta sa mabiyan a kwando.

Kara karanta wannan

Soyayya Ruwan Zuma, Yadda Wata Budurwa Ta Fada Tekun Lagas Akan Saurayi

Fitar da Muslimi dai, tsohon Gwamnan Jihar Barno Sen. kashim Shetima ya bar baya da kura, inda wasu ke murna, wasu kuma suna ganin an gefentar da kiristoci ne.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tinubu/Kashim
Za'a Maida Kiristocin Nigeria Saniyar Ware a Karkashen Takarar Musulmi da Musulmi Source: The Punch
Asali: UGC

EJoga yace

Wasu marasa kishin yan siyasa zasu yi amfani da duk wata hanya dan su ci zabe, ba tare da la'akarin shin hanyar zata cutar da wasu ba.
Yace kun ruguza kanku ta hanyar kin yin abinda ya kamata na bin yadda ake kowanne dan takara shugaba da mataimaki daga addini mabanbanta. amma kun karya tsarin siyasa, wanda san zuciyarku ne ya janyo, kuma muna mai tabbatar muku baku isa ku rusa addinin kiristanci ba.
Muna kira da duk wanda suke da karfarfan imani da su yi alwadare da wannan tsarin tare da kira kan yadda za'a gyara shi.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Ban Rufe Kofar Sulhu Ba, Atiku Ya Bawa Wike Amsa

Mai gabatar da jawabin taro a wajen, Prof. Josaiah Onaolapo, yace zaben shekarar 2023 zai iya zama barazana ga yan Nigeria da kuma tarnaku ga siyasar Nigeria muddin ba'aiwa kiristocin arewa dai-dai ba.

Yayin da yake jawabi kan makasudin taro mai take; siyasar yau: mafita ga kiristocin arewa, yace

Dole ne mabiya addinin kirista su shiga siyasa, domin bayan Allah sai siyasa kan tafiyar da kasa, idan dai mabiya adinin kirista zasu maida hanakli to da tuni bama cikin halin da muke ciki a yanzu. ya kamata ace mun farka daga baccin da muke

Onaolapo wanda ya bayyana cewa mabiya addinin na cikin tashin tsanani a yankin in anyi la'akari da yadda a cikin jihohi 19, uku ne kadaii suke mulki a cikinsu.

Ba jihar da zaka tarar da mabiya addinin kirista basu wuce kaso 30% ba, ciki har da jihohin Zamfara da sokoto, to mai muke da yawan namu. lokaci yayi da zamu canja.

Kara karanta wannan

Gwamna El-Rufa'i Ya yiwa Almajihar Sama Da 2500 Sha Tara Ta Arziki

Ga duk alamu zaben 2023 wata barazana ce ga mabiya addinin kirista musamman a arewa, muddin basuyi abinda ya kamata ba to kofa zata kulle musu.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida