An Damke Mai Tarban Bakin Yan Ta'addan ISWAP A Jihar Kaduna
- Hukumar Sojin Najeriya ta bayyana cewa ire-iren wadannan mutane ne manyan masu taimakawa yan ta'adda
- An damke daya daga cikin masu boye yan ta'adda a jihar Kaduna kan a turasu aikata hakkin ta'addanci
- Hedkwatar tsaro ta bayyana nasarorin da take samu wajen fittittikan yan ta'addan daga jihar Borno
Kaduna - Jami'an tsaro sun damke abokin aikin yan ta'addan ISWAP, Nasiru Mohammed, wanda ke tarban sabbin masu shiga kungiyar a yankin Arewa maso yammacin Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa an damke Nasiru ne a jihar Kaduna.
Masanin harkokin tsaro a tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya bayyana cewa an damkeshi bayan samun bayanai daga jama'a.
Majiyoyi sun bayyana cewa Nasiru dan kasuwa ne a kasuwar Central dake Kaduna kuma ya kasance mai baiwa yan ta'addan masauki.
Majiyoyin sun ce babban abinda ke hana jami'an tsaro kawar da yan ta'adda daga doro kasa shine ire-iren wadannan masu taimakawa musu da kai musu bayanai.
An damkashi hannun jami'an Sojin 1Div dak Kaduna don bincike.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’addan Boko Haram/ISWAP 60, Sun Kama Wasu Fiye da 90, DHQ
A wani labarin kuwa, Hedkwatar tsaro DHQ ta bayyana a ranar Alhamis 2 ga watan Nuwamba cewa, jami'an sojojin kasar sun yi ayyukan kakkabe 'yan ta'addan Boko Haram a yankin Arewa maso Gabashi.
Sanarwar da hedkwatar ta ce, sojoji sun hallaka akalla 'yan ta'adda 60 na Boko Haram/ISWAP jami'an , yayin da aka kama wasu 90 daga 'yan ta'addan.
Hakazalika, ta ce akwai sama da 'yan ta'adda 145 da suka mika kansu ga jami'an tsaro ciki har da mata da yara kanana a zagayen shiyyoyi shida na Najeriya, kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito.
Wannan na fitowa ne daga bakin daraktan yada labarai na gidan tsaro, Manjo Janar Musa Danmadami a taron bayyana nasarorin jami'an tsaro na kowane mako biyu da aka a makon nan.
Ya yi bayanin cewa, ayyukan da kuma nasarar da aka samu sun samu ne ta dalilin kara jajirewar jami'an tsaron da ke yakar ta'addanci a fadin kasar nan.
Asali: Legit.ng