Ba Zai Yiwu Mu Biya Lakcarori Kudin Aikin Da Basu Yi Ba, Ngige

Ba Zai Yiwu Mu Biya Lakcarori Kudin Aikin Da Basu Yi Ba, Ngige

  • Chris Ngige ya bayyana dalilin da yasa aka biya Malaman jami'o'in Najeriya rabin albashin Oktoba
  • Ministan na kwadago ya sake jaddada cewa gwamnati ba zata biya kudi watannin da Malaman ASUU sukayi yaji ba
  • Majalisar zartaswar ASUU ta yi taron gaggawa ranar Litinin domin duba yiwuwa sake koma yajin aiki

Abuja - Ministan Kwadago da Aikin, Chris Ngige, Yi ya watsi da rahotannin cewa ya saba alkawarin da yayi da ASUU biyo bayan biyan albashin rabin wata wa Malaman Jami'a.

A jawabin da mai magana da yawun ma'aikatar kwadago, Olajide Oshundun, ranar Asabar, yace babu gaskiya cikin zargin da ake masa, rahoton Tribune.

Yace albashin da aka biya Malaman ASUU na ranakun da suka yi aiki ne a watan Oktoba kuma ba rabi ba kamar yadda ake radawa.

A cewarsa, ba zai yiwu a biyashi kudin aikin da basu yi ba.

Kara karanta wannan

Tsaiko ga daliban Najeriya yayin da ASUU ke shirin komawa yajin aiki saboda dalili 1

Wani sashen Jawabin:

"Sakamakon hukuncin kotun daukaka kara da ta tabbatar da hukuncin kotun ma'aikatan Najeriya cewa ASUU ta koma bakin aiki, shugabannin ASUU sun rubutowa Minista wasika cewa an dakatar da yajin aiki."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sai Ministan ya aika wasika ma'aikatar kudi inda yayi umurnin cewa a dawo biyansu albashi. An biyasu kudin ranakun aikin da suka yi bayan kirga daga ranar da suka janye daga yajin aiki."
LEgit
Ba Zai Yiwu Mu Biya Lakcarori Kudin Aikin Da Basu Yi Ba, Ngige

Kungiyar Malaman Jami’a Ta ASUU Na Shirin Komawa Yajin Aiki

Yayin da daliban jami'a ke tsaka da doki da murnar komawa makaranta bayan watanni takwas suna zaune a gida saboda yajin ASUU, kungiyar ta ce za ta sake shiga yajin aiki.

Wannan na zuwa ne kasa da wata guda da kungiyar ta janye yajin aikin da ta fara tun watan Fabrairun bana, kamar rahotanni a baya suka bayyana.

Kara karanta wannan

Sauya Naira: Muna Sanye da Ido Kan Gwamnoni 3 Dake Karagar Mulki, Shugaban EFCC

Kungiyar ta ASUU ta koka kan yadda gwamnatin tarayya ta gaza cika alkawuran da ta dauka na gyara lamurran jin dadin malaman.

Mataimakin shugaban kungiyar ASUU, Dr Chris Piwuna, ya tattauna da BBC Hausa, inda ya bayyana musu halin da kungiyar ke ciki a yanzu.

Ya shaida cewa, ya zuwa yanzu dai kungiyar na shirin yanke shawarwari kan abubuwan da suka dace don kawo mafita ga bukatunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida