A Yayin Da Ake Rikicin Cire Koda, Kotu Ta Bawa FG Izinin Kwace Kadarorin Ekweremadu Guda 40, Duba Jerinsu

A Yayin Da Ake Rikicin Cire Koda, Kotu Ta Bawa FG Izinin Kwace Kadarorin Ekweremadu Guda 40, Duba Jerinsu

  • Babban kotun tarayya da ke Abuja ta bada umurnin kwace kadarori 40 na tsohon mataimakin shugaban majalisa, Ike Ekweremadu
  • Mai shari'a Inyang Ekwo, a hukuncinsa, ya umurci EFCC ta wallafa kadarorin a babban jaridar Najeriya cikin kwanaki 7
  • Kotun ta kuma umurci duk wani dan Najeriya da ke sha'awar siya ya bayyana hakan cikin kwana 14 bayan wallafa kadarorin kuma ya fada wa kotun dalilin da yasa ba za a kwace ba

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban majalisar tarayyar Najeriya, Sanata Ike Ekweremadu, wanda a halin yanzu yana Birtaniya, ya sake fuskantar wani kalubale.

A ranar Juma'a, 4 ga watan Nuwamba, babban kotu da ke zamanta a Abuja ta bada umurni na kwace filaye 40 mallakar sanatan, Nigerian Tribune ta rahoto.

Ekweremadu da EFCC
A Yayin Da Ake Rikicin Cire Koda, Kotu Ta Bawa FG Izinin Kwace Kadarorin Ekweremadu Guda 40, Duba Jerinsu. Hoto: EFCC
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

FG na Shirin Cin Basuka daga Chana, Fotugal da Turkiyya, Ta Bayyana Abinda Zata yi da Kudin

Mai sharia Inyang Ekwo, ya bada umurnin bayan karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1242/2020, da hukumar yaki da rashawa na EFCC ta rahoto.

Abin da ke faruwa a shari'ar Ekweremadu

Inyang Ekwo ya bawa hukumar umurnin ta wallafa kadarorin dan siyasan haifafan Enugu a babban jaridar kasa cikin kwana 7 da bada umurnin.

Alkalin ya ce duk wani da ke da sha'awar kadarorin da aka kwace ya sanar cikin kwana 14 bayan wallafa su a jarida, Daily Post ta rahoto.

Kotun, amma, ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 5 ga watan Disamban 2022, don sauraron mutanen da za su nuna ra'ayin mallakar kadarorin.

Jerin kadarorin Ekweremadu da EFCC za ta kwace

Gidaje 10 a Jihar Enugu

Gidaje 3 a Amurka (USA)

Gidaje 2 a Birtaniya (UK)

Gida 1 a Legas

Gidaje 9 a Dubai

Gidaje guda 15 a babban birnin tarayya Abuja

Kara karanta wannan

Yan Ta’adda Sun Dasa Bam Ta Karkashin Kasa a Kaduna, Mutum 2 Sun Halaka

Zargin Safarar Sassan Bil Adama: An Bukaci Birtaniya Ta Saki Ekweremadu Da Matarsa

A wani rahoto, kun ji cewa wasu yan Najeriya wadanda abin ke damunsu, sun roki gwamnatin Birtaniya ta bada belin tsohon mataimakin shugaban majalisar Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa, Beatrice, Daily Trust ta rahoto.

Sunyi wannan rokon ne karkashin wani kungiya mai suna 'Concerned Nigerians United for Ekweremadu and Family'.

Ana zargin cewa mata da mijin sun yi safarar wani matashi dan shekara 21 zuwa kasar Birtaniya don cire kodarsa su bawa 'yar su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164