Wani Mahaifi Ya Kashe Diyarsa Yar Shekara 20 Saboda Ta Kama Masa Mazantaka

Wani Mahaifi Ya Kashe Diyarsa Yar Shekara 20 Saboda Ta Kama Masa Mazantaka

  • Dakarun yan sanda sun cafke wani Magidanci kan zargin kashe ɗiyar cikinsa a kauyen Omum Unyiam ɗa ke jihar Akwa Ibom
  • A wata sanarwa da hukumar yan sandan ta fitar, tace wanda ake zargi yace diyar ce ta kama masa mazanta yayin wata gardama tsakaninsu
  • Kwamishinan yan sandan jihar ya yi kira ga ɗaukacin mazauna su kaucewa ɗaukar doka a hannu

Akwa Ibom - Hukumar yan sanda a jihar Akwa Ibom ta kama wani Magidanci, Sunday Etukudo, bisa zargin halaka ɗiyarsa Ofonmbuk Sunday, yar shekara 20 a kauyen Omum Unyiam, ƙaramar hukumar Etim Ekpo.

Channels tv ta ruwaito cewa mutumin yayi ajalin matashiyar budurwar ɗiyar tasa ne bayan wani saɓani y ashiga tsakaninsu a cikin iyali.

Kamen yan sanda.
Wani Mahaifi Ya Kashe Diyarsa Yar Shekara 20 Saboda Ta Kama Masa Mazantaka Hoto: Channelstv
Asali: Twitter

Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar yan sandan, Odiko Macdon, shi ne ya bayyan haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

'Mun Matsa Gaba' Atiku Ya Magantu Kan Yuwuwar Sasantawa da Su Wike Gabanin 2023

Yacce wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa mamaciyar ta damƙe masa mazantaka yayin da faɗa ya kaure tsakaninsu, hakan yasa ya mangareta da Sanda ta baje ƙasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ganin haka, magidancin ya ɓinne gawar ɗiyar a harabar gidansa dake kauyen Omum Unyiam, da nufin ɓoye laifinsa amma yan sanda sun tono gawar kuma sun ɗauketa domin gwaji.

Mista Macdon yace:

"Bisa bayanan da muka tattara, a ranar 9 ga watan Oktoba, 2022, da karfe 7:10 na dare, wani Sunday Etukudo ya kashe tare da binne diyarsa a harabar gidansa da ke ƙauyen Omum Unyiam."
"Mutumin yace wani saɓani ne ya taso a cikin gida har ta kai ga faɗa kuma ɗiyar ta damƙe masa mazantaka, shi kuma ya yi amfani da sanda ya mangareta."
"Sakamakon haka ne ta rasa rayuwarta kuma ya yanke shawarin ya ɓinne ta a harabar gidan domin lulluɓe wannan ɗanyen aikin da ya aikata."

Kara karanta wannan

'Na Gaji da Wannan Auren A Raba Mu' Wata Mata Ta Fada Wa Kotun Musulunci Cin Kashin da Mijinta Ke Mata

Wane mataki hukumar zata ɗauka?

Da yake tsokaci kan batun, kwamishinan yan sandan Akwa Ibom, Olatoye Durosinmi, ya umarci a gudanar da bincike mai zurfi kan Kes din. A cewara zasu gurfanar da wanda ake zargi nan ba da jimawa ba.

Ya kuma gargaɗi mutane su guji ɗaukar doka a hannu sannan ya rokesu da su kai rahoton duk wani saɓani wurin hukumar yan sanda

A wani labarin kuma wani magidanci Ya Fadi Yadda Ya Kama Matarsa Dumu-Dumu Tana Saduwa da Dan Uwansa, Ya Nemi Saki a Kotu

Wani Magidanci ɗan kasuwa, Justine Onu, ya nemi wata Kotu a Abuja ta raba aurensa da Joyce bisa zargin ganinta ta kwanta da ɗan uwansa.

Mutumin ya faɗa wa Alkali cewa matar bata kula da shi, yayansa da sauran iyalai, burinta kawai ta kwanta kowa ta samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: