Tinubu Ya Daukarwa Al’ummar Kogi Gagarumin Alkawari Gabannin Zaben 2023
- Al’ummar jihar Kogi za su yi sallama da annobar ambaliyar ruwa da ta addabi jihar daga 2023
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress ya ba mazauna jihar tabbacin shawo kan matsalar
- A cewar Bola Tinubu, annobar ambaliyar ruwa za ta zama tarihi da zaran ya dare kan kujerar shugaban kasa Buhari tare da Kashim Shettima
Kogi - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ya baiwa al’ummar jihar Kogi tabbacin cewa gwamnatinsa za ta magance matsalar ambaliyar ruwa idan har aka zabe shi a 2023.
Tinubu ya ce idan har ya zama shugaban kasa, matsalar ambliyar ruwa da ta addabi garuruwan jihar za ta zama tarihi.
Jaridar Punch ta rahoto cewa Tinubu ya dauki alkawarin ne a wani sakon fatan alkhairi da ya aikewa gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a ranar Alhamis, 3 ga watan Nuwamba a Lokoja, babban birnin jihar.
Da yake magana kan tanadin da ya yiwa jihar, tsohon gwamnan na jihar Lagas ya yarda cewa annobar ambaliyar ruwa a Kogi ba wai babban matsalar jihar bane kawai illa na Najeriya baki daya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
“Ambaliyar ruwa babbar matsala ce a Kogi watakila saboda ta kasance a tsakanin kogin Neja da Benue.
“Ambaliyar ruwa ta 'dai'daita wannan jaha a shekarar nan. Kun rasa rayuka masu muhimmanci, kun rasa dukiyoyi. Kun rasa gonaki. Daga cikin dalilan da yasa muka hada wannan tafiya ta musamman na Tinubu/Shettima don jan hankali ga wannan matsala ta ambaliyar ruwa.
“Ina mai fada maku a yau cewa ambaliyar ruwa za ta zama tarihi idan muka hau karagar mulki. Za mu yi aiki tare da gwamnatin jihar Kogi don bitar mafita maio dorewa ga wannan matsala. Bai kamata rahamar na mamakon ruwan sama ya zama annoba a kanmu ba."
Jaridar Vanguard ta kuma rahoto cewa Tinubu ya bayar da gudunmawar naira miliyan 100 ga wadanda ambaliyar ruwa ya ritsa da su a jihar ta Kogi.
Mun daina bacci har sai Tinubu da Shettima sun gaje Buhari, Matasan APC a arewa
A wani labarin, kungiyar matasan APC a arewa ta jinjinawa dan takarar shugaban kasa na APC da manyan jiga-jigan jam’iyyar kan zabar Sanata Kashim Shettima a matsayin wanda zai daga tutar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023.
Shugaban kungiyar Hon. Suleiman Liba ya bayyana cewa ba za su yi bacci ba har sai sun ga Tinubu da Shettima sun yi nasara a babban zaben mai zuwa, jaridar Vanguard ta rahoto.
Hon. Liba ya ce ya kamata yan Najeriya musamman mambobin jam’iyyar adawa su daina rura wutar fitina a siyasa ta hanyar cewa tikitin Musulmi da Musulmi na APC ba shine mafita ba.
Asali: Legit.ng