Gwamna Wike Ya Rantsar Da Sabbin Hadimai 100,000 Da Ya Nada
- Gwamna Nyesom Wike ya cika alkawarinsa na nada hadiman siyasa na musamman guda dubu dari
- Wike ya yi wadannan nade-nade ne a makonnin da suka gabata kuma aikinsu daya; kare kuri'un PDP a 2023
- Yan Najeriya sun bayyana mabanbantan ra'ayi kan wannan nadi da gwamna Wike yayi
Port Harcout - Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya rantsar da bari na farko na sabbin hadimai 100,000 da ya nada kan harkokin zabe wadanda zasu yi masa aiki a zaben 2023.
A taron da ya jagoranta ranar Alhamis, Wike ya rantsar da hadiman da zasu aiki a mazabun Kudu maso gabashin Rivers da Kudu maso yammacin jihar.
Gwamnan da kansa ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita.
Yace:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A Yau na rantsar da bari na farko na sabbin hadiman lamuran siyasa 100,000 da na nada a Kudu maso gabashin Rivers da Kudu maso yammacin Rivers."
Ana Saura Yan Watanni Ya Sauka: Nade-Nade Da Wike Yayi
Ana saura watanni takwas karewar wa'adin mulkinsa matsayin gwamna, Nyesom Wike na Rivers ya yi manyan nade-nade na dubunnan mutane lokaci guda.
Wannan ya biyo bayan rikice-rikicen da ke gudana tsakanin gwamnan da uwar jam'iyyarsa ta Peoples Democratic Party PDP.
A cikin wata guda kadai, Wike ya nada mutum kimanin dubu saba'in don kare muradun zaben da za'ayi a 2023.
A mukaman da ya bada, Wike ya sanya mutane a kowani lungu da sakon jihar don tsare masa akwatin zaben jiharsa gaba daya.
Bayan wadannan nade-nade, Wike dai ya bayyana cewa muddin ya raba jiha da jam'iyyar PDP babu yadda za'a yi ta lashe zabe.
Asali: Legit.ng