Allah Ya Yiwa Tsohon Dan Kwallon Kano Pillars, Bello KofarMata rasuwa

Allah Ya Yiwa Tsohon Dan Kwallon Kano Pillars, Bello KofarMata rasuwa

  • Daya daga cikin shahrarrun yan kwallo a jihar Kano da arewa ya rigamu gidan gaskiya jiya Talata
  • Ba'a bayyana takamammen cutar da Bello Kofarmata yayi fama da ita ba da tayi sanadiyar mutuwarsa
  • An haifi dan kwallon a shekarar 1988 kuma ya kwashe shekaru yana taka leda a gasar Firmiyar Najeriya

Allah ya yiwa Tsohon dan kwallon Super Eagles kuma Kano Pillars, Bello Musa Kofarmata, cikawa daren Talata, 2 ga watan Nuwamba, 2022.

Bello ya mutu ne yana dan shekaru 34 bayan jinyar da yayi a gidansa dake unguwar Kofarmata, Kano, rahoton Leadership.

Tsohon mataimakin shugaban kungiyar marubuta labaran kwallo a Najeriya SWAN, Ado Salifu, ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano.

Ya ce an yi jana'izarsa da safiyar Laraba a unguwar Kofarmata bisa koyarwan addinin Musulunci.

Kara karanta wannan

Sarakuna 17 Sun Yi Watsi da Atiku, Sun Karyata Batun Goyon Bayan Takararsa

Kofarmata ya na cikin gwanayen yan kwallon da suka taya Kano Pillars lashe gasar Firimiyar Najeriya a 2007/2008 inda yaci kwallaye 11 a kakar.

Shine mutum mafi yawan kwallaye a shekarar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kofarmata
Allah Ya Yiwa Tsohon Dan Kwallon Kano Pillars, Bello KofarMata rasuwa
Asali: Facebook

Bayan barin Kano Pillars a 2010, marigayin ya koma kungiyar kwallon Heartland a Owerri kafin komawa Elkanemi a 2012.

Bayan kankanin lokaci ya koma Kano Pillarsa sannan ya samu shiga kungiyar kwallon IK Start dake Norway.

Marigayin na cikin yan kwallon Najeriya U20 da suka taka leda a gasar kofin kwallon duniya da aka buga a Kanada 2007.

A 2010, ya bugawa Super Eagles wasar zumunta da Kongo guda a Abuja inda Najeriya ta lallasa DRC 5-2.

Yadda Dan Kwallon Najeriya Ya Nutse Bayan Ceto Fasinjojin 5 A Hatsarin Jirgin Ruwa Da Ya Ritsa Da Su

A wani labarin kuwa, Earnest Peremobowei, dan kwallon kafa, dan shekara 31 a nutse a Yenebelebiri a karamar hukumar Yenagoa bayan ceto mutane biyar da hatsarin jirgin ya ritsa da su.

Kara karanta wannan

Izalah ta yi kididdigan Masallatai da Makarantun ta, tace tanada 112,000

An gano gawar dan kwallon kwana biyu bayan hatsarin an kuma kai shi Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Yenagoa.

Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba da yamma lokacin da jirgin ruwa da suke amfani da shi don zuwa garinsu ya kife saboda karfin ruwa.

Marigayin ya lashe lambobin yabo masu yawa a gasa daban-daban na jihar ciki har da Internal Grace Football Club inda ya zama zakari a gasar kofin gwamnan jihar mai suna 'Prosperity Cup'.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida