Dalilin Da Yasa Nike Maulidi Duk Da Ni Kirista Ne: Fasto
- Fasto Yohana Buru ya shiga tattaki na musamman don Maulidin gidan Sheikh Abdullahi Mai Barota
- Malamin addinin na Kirista ya bayyana babban dalilin da yasa duk shekara ake Maulidi da shi
- Musulmai a fadin duniya kan yi murnar Maulidi a duk watar Rabiul Awwal na kalandar Musulunci
Kaduna - Shugaban Cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry, Kaduna, Fasto Yohana Buru, ya yi bayanin dalilin da ya sa yake murnar Maulidi tare da Musulmai a jihar.
Buru yace murnar Mauludi ba ta Musulmi bace saboda Annabi na kowa ne.
A cewarsa, akwai Musulmai dake taya su murnar bikin Kirismeti a Disamba kuma shi Maulidi ne ga Yesu AlMasihu.
Fasto Buru ya bayyana hakan ne a taron tattakin Maulidi da Malami Sheikh Abdullahi Mai Barota, ya shirya a unguwar Tudun Wada Kaduna, rahoton DailyTrust.
Yace a kowace shekara, ya kan halarci tarukan Maulidi 25 zuwa 30 a ciki da wajen Najeriya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yace:
"Mu Kiristoci ne kuma Littafinmu ya koyar da zama tare da 'yan uwanmu. Na yanke shawaran taya yan'uwana Musulmai murnar haihuwar Manzon musulunci, tsira ya tabbata a gareshi duk da cewa ni Kirista ne saboda Annabi Muhammadu (SAW) Musulmai suka fi so a fadin duniya."
"Wani dalilin kuma shine Musulmai na taya ni murnar haihuwar Yesu ranar Kirismeti a Cocina."
Wanda ya shirya tattakin Mauludi, Sheikh Abdullahi Mai Barota, yace sun gayyaci Kiristoci ne domin nuna zaman lafiya dake tsakaninsu.
Yace wannan zai karfafa zaman lafiya dake tsakanin mabiya addinan biyu.
Maulidi ba addini bane
Legit ta tuntubi malamin addini kuma Limamin Masallacin Alhaji Bello Damagun dake unguwar Unguwar Asokoro Abuja.
Ya bayyana nasa ra'ayin game da matsayar addini kan bikin Maulidi.
A takitaccen jawabin da yayi, yace yin bikin Maulidi ko tattaki don murnar ranar haihuwan Manzon Allah (SAW) ba koyarwan addinin Muslunci bane.
A cewarsa, wannan kirkirarren abu ne da aka yi a shekarun baya.
Yace:
"Wan nan Ba Musulunci Bane Kuma Baya Daga Cikin Shari'a Hasalima Bidia Ce da aka Kirkirota bayan Qarni Na 3 Lokacin Daular Fadimiyya Suka Kagoshi."
"Kuma Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam Kowani Kirkirenren Abu Cikin Shariya Bidia ne Yace Kowace Bidia Batace."
Asali: Legit.ng