Jirgin Buhari Ya Yi Tashiya Daga Koriya, Yana Hanyar Dawowa Gida

Jirgin Buhari Ya Yi Tashiya Daga Koriya, Yana Hanyar Dawowa Gida

  • Shugaban kasa ya kammala ziyarar aiki da ya kai kasar Koriya ta kudu kimanin mako guda da ya gabata
  • Shugaban kasan ya gana ga kungiyar yan Najeriya mazauna kasar Koriya gabanin tasowarsa
  • Shugaba Buhari ya tafi Koriya ranar Lahadi domin halartan taron ilmin hallitta na duniya 'World Bio Summit'

Jirgin Shugaba Muhammadu Buhari ya tashi daga babbar tashar jirgin Seoul, kasar Koriya ta kudu kuma yana hanyar dawowa gidan Najeriya.

Jirgin ya tashi ne da safiyar Juma'a, 28 ga watan Oktoba 2022.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jawabi a wajen bude taron harkokin lafiya na duniya da ke gudana a birnin Seoul, kasar Koriya ta Kudu.

Duk a taron, Gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta rattafa hannu kan yarjejeniya da gwamnatin kasar Koriya ta Kudu don gyara matatar man Kaduna.

Kamfanin man feturin Najeriya NNPCL da Kamfanin man feturin Koriya Daewoo suka rattafa hannunkan yarjejeniyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimin Buhari kan gidajen rediyo da talabijin, Buhari Sallau, ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita.

Daga cikin wadannan ke hallare a taron akwai COO Daewoo E&C Seung-II Cho, Shugaban kamfanin Daewoo E&C Mr. Jungwan Baek, da Mr. Won Ju Jung,

Sauran sune Jakadan Najeriya zuwa Koriya ta kudu, Amb Ali Magashi; Mininstan Mai Timipre Sylva da Shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari.

Hakazalika akwia Ministan Lafiya, Osagie Ehanire; Ministan harkokin wajen Najeriya, Geofrey Onyeama; Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari.

Tafiyar Buhari Koriya

Ana gudanar da taron mai taken ‘World Bio Summit’ ne a yau Talata, 25 ga watan Oktoba.

Kamar yadda muka bayyana a baya, wannan shine karo na farko da kungiyar lafiya ta duniya da gwamnatin Koriya ke shirya irin wannan taro.

A ranar Lahadi, 23 ga watan Oktoba ne dai jirgin shugaban kasar ya tashi daga filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke babbar birnin tarayya Auja zuwa kasar ta Koriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel