Gini Ya Danne Mutanen da Ambaliyar Ruwa Ta Raba da Gidajensu a Kogi, Rayuka Sun Salwanta
- Al'ummar yankin Ayah da ke karamar hukumar Ibaji a jihar Kogi sun wayi garin Alhamis cikin bakin ciki
- Ginin bene ya ruso kan wasu mutane da ke samun mafaka a sansanin Ayah sakamakon ambaliyar ruwa da ta rabo su da gidajensu
- Mutum biyar sun kwanta dama yayin da aka kwashi wasu da dama da suka jikkata zuwa asibiti don jinya
Kogi- Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa akalla rayuka biyar ne suka salwanta bayan wani ginin bene ya ruguzo kan mutanen da ambaliyar ruwa ta raba da gidajensu a Ayah da ke karamar hukumar Ibaji a jihar Kogi.
An tattaro cewa lamarin ya afku ne a safiyar ranar Alhamis, 27 ga watan Oktoba a garin Ayah.
Jami'in kula da ci gaban karamar hukumar Ibaji, Mista Onalo Achimugu, ya bayyana cewa mamatan sun kasance mata hudu da namiji daya.
An rahoto cewa mutanen na samun mafaka ne a ginin benen inda suke jiran ambaliyar ruwan ta kafe kafin su koma gidajensu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Achimugwu ya ce:
"Da misalin karfe 1:00 na tsakar daren yau, wasu daga cikin mutanen da ambaliyar ruwa ta ritsa da su a karamar hukumar Ibaji da ke zaune a wani ginin bene a sansanin Ayah, sun rasa rayukansu yayin da wasu suka jikkata."
Ya bayyana cewa da izinin shugaban karamar hukumar, Iko-Ojo Obiora, an kwashi wasu da suka jikkata zuwa Irrua a jihar Edo, sannan wasu na Idah inda suke samun kulawar likitoci.
Obiora ya kuma tabbatar da lamarin yana mai cewa "biyar sun mutu sannan da dama sun jikkata."
Yadda Dan Kwallon Najeriya Ya Nutse Bayan Ceto Fasinjojin 5 A Hatsarin Jirgin Ruwa Da Ya Ritsa Da Su
Ya bayyana cewa an kwashi wadanda suka jikkata zuwa asibitoci mafi kusa.
2023: Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Dakatar da Yakin Neman Zabe Kan Abu Daya
A wani labarin, Obi, ya dakatar da yakin neman zaɓen 2023, Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Obi ya sanar da wannan matakin ne yayin da ya ziyarci gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ranar Laraba a babban birnin tarayya Abuja.
Ɗan takarar ya ɗauki wannan matakin ne a dai-dai lokacin da Ambaliyar ruwa ke ci gaba da jawo hasarar rayuka da dukiyoyi a jihohin ƙasar nan.
Asali: Legit.ng