Da Duminsa: CBN Zata Sake Tsarin Wasu Takardun Kudin Najeriya
- Babban bankin Najeriya, CBN ya bayyana cewa zai sauya fasalin wasu takardun kudin Najeriya nan da ranar 15 ga watan Disamban 2022
- Gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele ya bayyana cewa Buhari ya amince da sauya N200, N500 tare da N1000 ta kudin Najeriya
- Ya sanar da cewa daga ranar da sabbin kudin suka fita, ‘yan Najeriya zasu iya kai tsoffin bankuna domin a musanya musu da sabbin
FCT, Abuja - Babban bankin Najeriya a ranar Laraba, 26 ga watan Oktoban 2022 ya bayyana cewa zai sauya tsarin wasu kudin Najeriya.
Gwamnan babban bankin Najeriyan, Godwin Emefiele ya bayyana hakan ga manema labarai a garin Abuja, Channels TV ta rahoto.
Babban bankin Najeriyan yace zai sauya tsarin N200, N500 da N1000 kuma sabbin kudaden zasu fita daga ranar 15 ga watan Disamban 2022.
An dauka wannan matakin ne domin kayyade kudin dake yawo tsakankanin jama’a kamar yadda shugaban CBN ya bayyana.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shugaban CBN din ya bayyana cewa, ya samu amincewa shugaban kasa Muhammadu Buhari domin fitar da sabbin kudin tare da maye gurbinsu.
Bayan an fitar da sabbin kudaden, ‘yan Najeriya zasu iya kai tsofaffin bankuna don a musanya musu da sabbi.
Gwamnan babban bankin ya bayyana damuwarsa kan yadda ake adana kudade a Najeriya.
Kamar yadda yace, da yawan kudaden kasar sun wajen ma’adanar bankuna kuma CBN ba zata lamunci hakan ya cigaba ba.
“A bayani mai kyau, zuwa karshen watan Satumban 2022, kiyasi ya bayyana cewa N2.7 tiriliyan daga cikin N3.3 tiriliyan dake yawo a kasf nan basu cikin ma’adanar bankunan kasar nan amma sun hannun jama’a.”
- Yace.
Shugaba Buhari ya kaddamar da kudin e-Naira tare da Gwamnan CBN
A wani labari na daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da kudin intanet na Najeriya, e-Naira, ranar Litinin, 25 ga Oktoba, a fadar Aso Villa dake birnin tarayya Abuja.
Wadanda ke hallare a taron kaddamar da kudin sun hada da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo; Gwamnan bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele.
CBDC wakilci ne na tsarin kudaden intanet masu cikakken iko da ake samar da su kamar yadda Babban Banki ke samar da kudi gama-gari.
Asali: Legit.ng