Najeriya Ce Ta Farko: Cikakken Jerin Kasashen Da Dubai Ta Hana Shiga Kasarta

Najeriya Ce Ta Farko: Cikakken Jerin Kasashen Da Dubai Ta Hana Shiga Kasarta

Ma'aikatar Shiga da Fice ta Kasar haddadiyar daular Larabawa watau UAE ta haramtawa 'yayan wasu kasashen Afrika shiga kasarta gaba daya, Najeriya ce ta farko.

Gwamnatin UAE ta sanar da hakan ne ranar Juma'ar da ta gabata a sakon da ta aikewa gwamnatocin kasashen cewa babu wanda zata sake baiwa Biza, a cewar BBC.

A wasikar sanarwar da gwamnatin ta yiwa abokan huldanta irinsu kamfanonin jirage da dillalan tafiya, gwamnatin kasar ta ce daga yanzu duk wanda ya nemi biza ba za'a bashi ba.

Buhari
Najeriya Ce Ta Farko: Cikakken Jerin Kasashen Da Dubai Ta Hana Shiga Kasarta Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Tace:

"Muna sanar da ku cewa kada ku bada bizan kwanaki 30 ga yan wadannan kasashe daga ryau 18 ga Oktoba, 2022. Kada a sake karban takardan neman bizan wani."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Jerin Abubuwa 7 Da Ka Iya Faruwa Da Mutum Idan Ya Ziyarci Jihohin Najeriyan Nan 14: Amurka Tayi Gargadi

Ga jerin kasashen:

  1. Najeriya
  2. Ghana
  3. Uganda,
  4. Sierra Leone,
  5. Sudan,
  6. Cameroon,
  7. Liberia,
  8. Burundi,
  9. Republic of Guinea,
  10. Gambia,
  11. Togo,
  12. Senegal,
  13. Benin,
  14. Ivory Coast,
  15. Congo,
  16. Rwanda,
  17. Burkina Faso,
  18. Guinea Bissau,
  19. Comoros
  20. Dominican Republic.

Hana Yan Najeriya Zuwa Dubai: Gwamnatin Tarayya Ta Caccaki Kasar UAE

Manyan Jami'an Gwamnatin Najeriya sun yi Alla-wadai da haramta baiwa yan Najeriya Biza da kasar UAE tayi.

Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana bacin ransa bisa haramtawa yan Najeriya Biza da Gwamnatin kasar UAE tayi.

Emefiele yace Najeriya babbar kasa ce na kasuwanci kuma gwamnatin Dubai ta daina yi mata barazana.

Shi kuwa Ministan Sufurin Jirgin Sama, Hadi Sirika, yace ko a jikinsa idan gwamnati UAE ta hana yan Najeriya shiga kasarta.

Sirika yace duk da cewa akwai kudaden jiragen sama kasar waje da ba'a biyasu ba, bai kamata kasar Dubai ta rika yiwa yan Najeriya barazana ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Manyan Kantunan Abuja Sun Fara Rufewa Sakamakon Labarin Cewa Za'a Kai Hari

A cewarsa:

"Idan kuna da matsala da mu, zuwa ya kamata kuyi mu zauna, mu tattauna kuma mu baku abinda ke hannunmu kafin mu gama biya."
"Abinda ke da ban haushi shine barazanar da ake yi. Kowace kasa yanzu sai ta fara yiwa Najeriya barazanar hanata shiga kasar, hana jama'arta Biza."
"Ba zasu yi aiki ba, zasu rufe Legas da Abuja. Su sani fa akwai kasashen da aka yi hannun riga da su kuma sun rayuwa lafiya lau."
"Akwai misalai a Asiya, kasashen larabawa, ha da Turai. Ba tsoro muke ji ba. Haka ma gyara zai sa muyi idan muka ji uwar bari."

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida