Shugaba Buhari Ya Kai Ziyara Fadar Shugaban Kasar Koriya, Anyi Zaman Diflomasiyya

Shugaba Buhari Ya Kai Ziyara Fadar Shugaban Kasar Koriya, Anyi Zaman Diflomasiyya

  • A kwana na biyu a ziyarar aiki da ya kai kasar Koriya, Shugaba Buhari ya gana da shugaban kasar
  • Tawagar Najeriya karkashin Buhari tayi zaman diflomisyya da tawagar shugaban kasar Koriya
  • Shugaba Buhari ya tafi Koriya ranar Lahadi domin halartan taron ilmin hallitta na duniya 'World Bio Summit'

Seoul - Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyara ta musamman fadar shugaban kasar Koriya ta kudu dake birnin Seoul a ranar Laraba, 26 ga watan Oktoba, 2022.

A ziyarar, shugaba Buhari ya gana da shugaban kasa, Yoon Suk-Yeol, inda akayi zaman Diflomasiyya.

Hadimin Shugaban kasa, Buhari Sallau, ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita inda ya skai hotunan ziyarar da Shugaban kasan ya kai.

Buhari
Shugaba Buhari Ya Kai Ziyara Fadar Shugaban Kasar Koriya, Anyi Zaman Diflomasiyya Hoto: @Buharisallau1
Asali: Twitter

Yace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Hotuna: Shugaba Buhari Ya Yi Jawabi a Wajen Bude Taron Lafiya Na Duniya Da Ke Gudana a Koriya Ta Kudu

"Shugaba Muhammadu Buhari ya yi zaman diflomasiyya da Shugaban jamhuriyyar Koriya a fadar shugaban kasan Koriya ranar 26 ga Oktoba, 2022."

Wadanda ke hallare a zaman sun hada Shugaban kamfanin mai na NNPCL, Mele Kolo Kyari; Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffey Onyeama, dss.

Shugaba Buhari Ya Yi Jawabi a Wajen Bude Taron Lafiya Na Duniya Da Ke Gudana a Koriya Ta Kudu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jawabi a wajen bude taron harkokin lafiya na duniya da ke gudana a birnin Seoul, kasar Koriya ta Kudu.

Ana gudanar da taron mai taken ‘World Bio Summit’ ne a yau Talata, 25 ga watan Oktoba.

Hadimin shugaba Buhari kan harkokin sadarwan zamani, Buhari Sallau ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.

Kamar yadda muka bayyana a baya, wannan shine karo na farko da kungiyar lafiya ta duniya da gwamnatin Koriya ke shirya irin wannan taro.

Kara karanta wannan

‘Dan Takaran PDP a Zaben 2023, Ya Cire Gabar Siyasa, Ya Yabi Shugaba Buhari

A ranar Lahadi, 23 ga watan Oktoba ne dai jirgin shugaban kasar ya tashi daga filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke babbar birnin tarayya Abuja zuwa kasar ta Koriya.

Hadimin Buhari Ya Caccaki Peter Obi Kan Kaiwa Dubban Jama’a Tallafin Sunki 24 na Biredi

A gefe guda, Bashir Ahmad, mai bai wa shugaban kasan shawara kan sadarwa mai dogaro da fasahar zamani, ya zolayi Peter Obi, ‘dan takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar LP, kan tallafin da ya bai wa wadanda ambaliyar ruwa ta ritsa dasu a jihar Anambra a baya-bayan nan.

A wata wallafa da yayi a shafinsa na Twitter a ranar Asabar, Obi ya bayyana wasu kayayyaki da ya bai wa mazauna yankin Ogbaru dake jihar Anambra da ‘yan gudun hijira a sansanin Atani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel