Tsadar Mai: N200 Zamu Fara Sayar Da Litan Mai, Kungiyar IPMAN
- Tsadar mai na cigaba da tsananta a fadin tarayya musamman a birnn tarayya Abuja da Legas
- Kungiyar IPMAN yankin kudu maso yamma ta bayyana cewa mambobinta ba zasu dau asara ba gaskiya
- Hukumar NMDPRA ta ce yan Najeriya su kwantar da hankulansu akwai isasshen man fetur a ajiye
Direbobi da masu hawa motocin haya sun koka game da tsada da wahalar mai da ake fama da shi a birnin tarayya Abuja, jihar Legas da wasu jihohin kudu maso yamma.
Motoci sun cika gidajen mai yayinda direbobin tasi suka kara farashin kudin mota saboda tsadar man.
Wasu fasinjojin yanzu sun koma takawa da kafafuwansu saboda wahalar da aka shiga.
Kawo yanzu an fara sayar da litan man fetur N200 a jihohin Legas, Ogun, Oyo, yayinda wasu gidajen mai ke sayarwa N250 a Abuja sabanin N175 da gwamnati tace a sayar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kungiyar yan kasuwan mai masu zaman kansu na IPMAN yankin kudu maso yamma ta ce ana samun matsalar ne sakamakon rashin samun mai daga wajen kamfanin man Najeriya NNPC, rahoton TheNation.
Ta ce yanzu N178 suke dauko litan mai daga depot sabanin N145.
IPMAN yace ko kadan ba zai yiwu mambobinta su cigaba da sayar da mai N175/N180 ba.
Shugaban IPMAN na yankin, Dele Tajudeen, a jiyar ya laburta cewa:
"Babu depot din NNPCL dake da man fetur. Masu Depot na zaman kansu suna amfani da hakan don kara farashin mai. Bamu da wani zabi illa saya daga wajensu."
"Bamu yarda da karin farashin mai ba amma ba zamu dau asara ba. Mambobinmu basu da wata zabi illa sayar da litan mai N185 zuwa N200 a Legas, Ogun da Oyo. A Kwara, Ondo, Osun da Ekiti kuma N200 zuwa N210."
Muna da isasshen mai, NMDPRA
A rahoton hukumar NMDPRA na baya-bayan nan, ta nuna cewa akwai isasshen man fetur da zai isa Najeriya na kusan wata guda.
A rahoton dake shafinta na yanar gizo, hukumar tace tana da litan mai 1,546,880,583 a ajiye.
Asali: Legit.ng