Yanzu Yanzu: Allah Ya Yiwa Hadimin Gwamnan Nasarawa Rasuwa
- Mai ba gwamnan jihar Nasarawa shawara kan ayyuka na musamman, Alhaji Murtala Lamus, ya kwanta dama
- Alhaji Lamus ya rasu ne a yau Talata, 25 ga watan Oktoba, kuma tuni aka sada shi da gidansa na gaskiya
- Gwamna Sule wanda ya nuna kaduwarsa da samun labarin ya yi addu'an samun jin kan Ubangiji ga mamacin
Nasarawa - Allah ya yiwa mai ba Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa shawara kan ayyuka na musamman, Alhaji Murtala Lamus, rasuwa a ranar Talata, 25 ga watan Oktoba.
Babban sakataren labaran Gwamna Sule, Ibrahim Addra ne ya tabbatar da rasuwan Lamus a cikin wata sanarwa da ya fitar, Sahara Reporters ta rahoto.
Sanarwar ta bayyana cewa kafin mutuwar Lamus, ya kasance babban dan siyasa wanda ke dauke da soyayyar jihar Nasarawa da al’umma a zuciya.
Gwamna Sule ya nuna kaduwa da samun labarin mutuwar hadimin nasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan na Nasarawa wanda ya sallaci gawar marigayin ya je har makabarta inda aka sada shi da gidansa na gaskiya, jaridar Independent ta rahoto.
Ya roki Allah ya ji kan marigayi Lamus yasa ya huta sannan ya baiwa yan uwa da abokansa juriyar wannan rashi da suka yi.
Allah Ya Yiwa Dan Tsohon Ministan Buhari Rasuwa
A wani labari makamancin wannan mun ji cewa Allah ya yiwa dan tsohon ministan wasanni Solomon Dalung, Nehemiah Dalung, rasuwa yana da shekaru 33 a duniya.
Nehemiah ya mutu ne a safiyar ranar Litinin, 24 ga watan Oktoba, bayan ya yi fama da matsananciyar rashin lafiya.
Mahaifinsa, Dalung ne ya sanar da labarin mutuwar tasa a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook yana mai tawali’u ga ubangiji.
Ya rubuta a shafin nasa:
“Duk da cewar rayuwar Nehemiah ta zo karshe kafin mu shirya mata, ba za mu taba mantawa da rayuwar da yayi da mu ba. Shekarun Nehemiah Dalung 33. Dana ne shi. Babu wata kalma da za ta nuna irin radadi da bakin cikin rasa da a yayin da yake ganiyar samartaka, amma mun fawwalawa Allah mai bayarwa da karba. Allah ya ji kansa.”
Asali: Legit.ng